Gwamnatin Buni Ta Gudanar Da Muhimman Ayyukan Raya Kasa A Shekarar 2021..inji Lamin

0
371


Sani Gazas ChinadeDaga Damaturu
Bisa ga kudirinta na cimma muhimman nasarori ta bangarori da dama kan ayuukan raya kasa a shekarar 2021 gwamnatin Mai Mala Buni ta Jihar Yobe ta gudanar da ayyukan raya kasa masu dimbin yawa da suka taba rayuwar al’umma kai tsaye.

A Bayanin da ya yi ga manema labarai a Sakatariyar Kungiyar ‘Yan Jaridu ta kasa NUJ reshen Jihar Yobe a ranar Jumu’a kwamishina ma’aikatarma’aikatar yada labarai da harkokin cikin gida na Jihar Alhaji Muhammad Lamin ya bayyana cewar, cikin shekarar 2021 gwamnatin Buni ta gudanar da muhimman ayyuka kan abin da ya shafi ayyukan raya kasa ta kowane bangare na rayuwar al’umma.
Kwamishinan ya kara da cewa, in an duba bangaren shimfidawa hanyoyin mota birni da karkara a cikin shekarar 2021 sun kammala da Gina sababbin hanyoyin da suka hada da ta Balanguwa zuwa Kumaganam mai Nisan kilomita 46 a kananan hukumomin Nguru da Yusufari sai kuma hanyar da a yanzu ake shimfidawa Daga Danchuwa zuwa Bula ta wuce Garin Bingel mai nisan kilomita 12.5 da kuma sake gyara hanyar da ta tashi daga Damaturu fadar Jihar zuwa garin Buni Gari mai nisan Kilomita 50km  tare kuma da shimfidawa hanyoyin mota a cikin manyan garuruwan Jihar da suka hada da hada da Damaturu, Potiskum da sauran su.

Har ila yau kuma akwai sake gyara hanyar da ta tashi daga Jaji-maji zuwa Karasuwa mai nisan kilomita 25.5 sai kuma hanyar da ta tashi daga Damaturu fadar Jihar zuwa Buni-Gari Mai nisan kilomita 50, tare da shimfida hanyoyi a wasu manya-manyan garuruwan Jihar da suka hada da Damaturu fadar Jihar da Potiskum da sauran su.

“Bayan Samar da hanyoyi kuma, kwamishinan ya kara da cewa, ta bangaren Samar da ruwan sha wadda sai da shi ne rayuwa ke inganta gwamnatin ta daga daraja wasi rikiyoyin famfon daga kananan rijiyoyi ya zuwa manya a garuruwan Ngurmai, Shishiwaji da kuma wasu rijiyoyin a kananan hukumomin Gujba, Bade da Fika.”

Har wayau kuma suna  kuma kara fadada aikin ruwan Buni Gari don samun ruwan sha a wadace dai-dai da bukatun al’umomin yankin.

Dangane da harkokin ruwan shan aikin ruwan nan na Damaturu mai dogon tarihi a yanzu haka ya samu sahalewa wannan gwamnatin wadda aka fara aikin gadan-gadan don kaiwa ga nasara a wannan karon, wadda cikin kankanin lokaci zai kammalu da izinin Allah.

Kan harkokin sufuri da wutar lantarki kuwa nan ma a cewar kwamishinan. a halin yanzu gwamnatin Buni ta sake inganta wutar lantarki a wasu rukunon gidajen ma’aikatar guda 3 cikin garin Damaturu da suka hada da Sani Daura, Ben Kalio da Dabo Aliyu, kana an kuma hada wasu kauyuka da babban layin wutar lantarki ta kasa tare da da wutar lantarki mai amfani da hasken rana a rukunin gidajen Don Etibet da sansanin horar da ‘yan gudin hijira fake Dazigau.

Kan abin da ya shafi sufuri kuwa tunin aikin nan na gina sabon filin jirgin saman daukar kaya na kasa da kasa na gab da kammaluwa tare da wadata shi da kayayyaki na zamani iri-iri. Kana gwamnatin ta kuma sayo motoci kirar Toyota Bus guda 20 ga kamfanin sufuri na Jihar Yobe Line don kawo sauki ga al’umma.

“Ta bangaren tattalin arziki da kasuwanci kuwa tun tunin gwamnatin Buni ta kaddamar tare da gina kasuwanni na zamani a garuruwan Damaturu, Potiskum, Nguru da Gashuwa wadda tunin aka kammala ta. Sai kuma kokarin tada wasu kamfanonin da ada suka durkushe kamar kamfanin samar da takin zamani don manoma na Gujba da kuma kamfanin sarrafa leda dake Damaturu.” 

Ta bangarorin kiwon lafiya, Ilimi, aikin gona da sauran bangarori nan ma gwamnatin Mai Mala ta taka muhmman nasarori ma su dimbin yawan gaske.

Leave a Reply