Wani Ya Kashe Matarsa Da Duka

0
690

Mustapha Imrana Abdullahi

Wani mutum mai shekaru 27 mai suna Yusuf Zubairu ya doki  matarsa da sanda wanda sanadiyyar hakan matar ‘yar shekaru 23 mai suna Fatima Harso ta mutu har lahira.

An dai bayyana cewa Zubairu ya kasa danner fushinsa wanda sanadiyyar hakan ya halaka da matarsa a ranar Laraba 29 ga watan Disamba 2021.

 Wata shaidar gani da ido da ta kasance makwabciya ga ma’auratan biyu, mai suna Rabi Lawan, wadda ta yi kokarin raba su lokacin da suke fadan ita ma ta samu kanta cikin wani hali sakamakon dukan da ya sha ita ma daga wurin Zubairu lokacin da suke fada da matarsa idonsa a rufe.

Da yake yi wa manema labarai bayani mai magana da yawun rundunar yan sandan Jihar Kano Lawal Adam, ya bayyana irin yadda ita shaidan gani da ido ya shaida masa mai shekaru 65 Bulama Muntari Ubale cewa ya yi, ” Zubairu ya doki matarsa ne da wata sanda a kanta lokacin da suke fada da matar tasa, wanda sanadiyyar hakan ya yi sanadiyyar rasa ranta”, ya kara da cewa wata matar da ta je domin rabon fadan ita ma ta samu jin rauni a jikinta. 

 Da jami’an tsaron Yan Sanda suka samu labarin mai magana da yawun su ya ce nan da nan aka tura jami’ansu zuwa wurin da abin ya faru wato kauyen Baldi, da ke karamar hukumar Sule Tankarkar a cikin Jihar Jigawa kuma an dauki mutane biyu da lamarin ya rutsa da su zuwa babban asibitin Gumel inda a nan ne jami’an lafiya suka tabbatar da mutuwar matar Zubairu.

Kamar yadda mai magana da yawun rundunar Yan Sandan ya ce wadda ta ji rainin na can asibitin ana duba lafiyarta, ya zuwa lokacin ganawa da manema labaran.

Ya kara da cewa tuni wanda ake zargin ya shiga komar jami’an tsaron Yan Sanda.

Leave a Reply