Gwamnatin Aljeriya ta karrama limamin nan, Imam Walid Mehsas wanda kyanwa ta hau jinkinsa a daidai lokacin da yake jagorantar Sallar Taraweeh, inda cikin tausaya wa ya yi ta shafar kyanwar wadda ta sumbace shi kafin daga bisani ta sauka daga jikinsa don raɗin kanta.
KU KUMA KARANTA: ‘Yan mata uku sun tsere a lokacin da ake ƙoƙarin safarar su zuwa ƙasar Libya
Wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta ne ya nuna yadda Imam Walid ya mu’amalanci kyanwar cikin kyawun yanayi, lamarin da ya ƙayatar da jama’a da dama hatta waɗanda ba Musulmai ba daga sassan duniya.
Limamin ya sha yabo da jinjina, yayin da manyan kafafen yaɗa labarai na duniya suka yi ta yaɗa wannan labarin.
Yanzu haka gwamnatin Aljeriya ta gayyace shi tare da shirya masa taron liyafa na musamman, inda Ministan Kula da Lamurran Addini na ƙasar, Dr. Youssaf Belmahdi ya yaba masa kan wannan kyakkyawar ɗabi’ar da ya nuna wa dabba.
[…] KU KUMA KARANTA: Gwamnati ta karrama limamin da ya tausaya wa kyanwar da ta hau kansa a sahun sallah […]
[…] KU KUMA KARANTA: Gwamnati ta karrama limamin da ya tausaya wa kyanwar da ta hau kansa a sahun sallah […]