Gwamna Yobe ya je ta’aziyyar rasuwar mahaifiyar Gwamnan Katsina

0
21
Gwamna Yobe ya je ta'aziyyar rasuwar mahaifiyar Gwamnan Katsina

Gwamna Yobe ya je ta’aziyyar rasuwar mahaifiyar Gwamnan Katsina

Daga Ibraheem El-Tafseer

Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni ya je ta’aziyya ga takwaransa na Jihar Katsina, Gwamna Dikko Umar Radda, gwamnati da al’ummar jihar bisa rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Safara’u Umaru.

Gwamna Buni tare da Gwamnan Jihar Sakkwato, Alh. Ahmed Aliyu, da Mataimakin Shugaban Ƙasa na Musamman kan Harkokin Siyasa da Sauran Al’amura, Alh. Kabiru Masari, sun yi addu’a ga Allah Ya gafarta mata kura-kuranta, Ya kuma ba ta Aljannatul Firdausi.

KU KUMA KARANTA:Allah ya yiwa fitaccen attajiri a Kano Alhaji Nasiru Ahali rasuwa

Gwamna Buni ya bayyana rasuwar marigayiya Hajiya Safara’u a matsayin babban rashi ga iyalanta, al’ummarta da Jihar Katsina gaba ɗaya.

“Ta rasu a lokaci mai matuƙar muhimmanci da ake buƙatar shawarwari da hikimarta, kuma za a ci gaba da tuna ta saboda goyon bayanta, jagorancinta da kuma kyautatawarta,” in ji Gwamna Buni.

Haka kuma, ya yi addu’a ga Allah Ya bai wa iyalan mamaciyar da al’ummar Jihar Katsina haƙuri da juriyar wannan babban rashi.

Leave a Reply