Wane ne marigayi Galadiman Kano Abbas Sanusi?
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Marigayi Alhaji Abbas Sunusi shi ne Ɗan majalisar Sarki mafi daɗewa a masarautar Kano, Abbas Sanusi, ya rasu ya na da shekaru 92.
Marigayi yarima, wanda shi ne Galadiman Kano, muƙami mafi girma a majalisar Sarki, ya rasu ne a jiya Talata, 1 ga Afrilu, a Kano, bayan ya sha fama da jinya.
Abbas Sanusi, wanda ya taba zama dan Majalisar Masarautar Kano kafin samun ‘yancin kai, mahaifinsa, Sarki Sanusi na daya ya nada shi a matsayin Sarkin Dawakin Tsakar Gida da Hakimin Ungogo a 1959.
Ya zama Dan Iyan Kano a 1962 a zamanin Sarki Muhammadu Inuwa, sannan kuma a zamanin Sarki Ado Bayero ya zama Wamban Kano.
Ya samu matsayi mafi girma na Galadiman Kano a zamanin mulkin dan uwansa Sarki Muhammadu Sanusi II.
KU KUMA KARANTA:Galadiman Kano Abbas Sanusi, ya rasu yana da shekaru 92
An haife shi a 1933 a garin Bichi, inda marigayin ya fara karatunsa a makarantar Elementary ta Kofar Kudu a 1944 kuma ya halarci makarantar Midil ta Kano (Kwalejin Rumfa a yau) a 1948.
Daga cikin ‘ya’yansa akwai Abdullahi Abbas Sunusi, shugaban jam’iyyar APC na yanzu, kuma mahaifi ga Muhmoud Abbas Sunusi (walidin Kwankwasiyya) mataimaki na musamman ga Gwamnan Kano, kan harkokin masarautu.
Za’ayi Sallar Jana’izarsa a Fadar Sarkin Kofar Kudu, amma har yanzu ba a fadi lokaci ba.
A madadin Jaridar Neptune Prime na mika sakon ta’azziyar ta ga iyalai da Yan da al’ummar Kano dafatan Ubangiji ya yi masa rahama