Gwamnan Yobe ya biya bashin Naira biliyan 39, ya jaddada tsare-tsaren tattalin arziƙi
Gwamnatin jihar Yobe ƙarƙashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni ta biya bashin Naira biliyan 39 daga cikin Naira biliyan 96 da aka karba daga cibiyoyin hada-hadar kuɗi a faɗin ƙasar nan cikin shekara ɗaya.
Wannan bayani ya fito ne daga shugaban sashen kula da basussuka na ma’aikatar kuɗi ta jihar Yobe, Malam Muhammad Rabiu Ibrahim, yayin taron masu ruwa da tsaki na jihohi da kuma babban taron Majalisar Jama’a da aka gudanar a Damaturu.
Taron wanda majalisar kula da kyautata yanayin kasuwanci ta shugaban ƙasa (PEBEC) ta shirya, an gudanar da shi ne domin nazarin nasarorin da jihar Yobe ta samu wajen aiwatar da sauye-sauyen da ke inganta harkokin kasuwanci da kuma daidaitawa da tsare-tsaren tattalin arziƙin ƙasa.
KU KUMA KARANTA: Gwamnan Yobe ya fi kowane Gwamna kula da harkar kiwon lafiya a jiharsa – Jaridar Blueprint
A cewar Malam Ibrahim, biyan bashin da ya shafi tsakanin zangon farko na shekarar 2024 zuwa zangon farko na 2025, ya nuna cikakken ƙudurin Gwamna Buni na tabbatar da daidaiton tattalin arziƙi, riƙon amana a harkokin kuɗi da kuma ƙara janyo hankalin masu zuba jari.
Ya ce gwamnatin Buni ba kawai tana rage bashin da ke kanta ba, har ila yau ta ɗauki tsauraran matakai wajen sanya ido kan karɓar sabbin bashi. “Duk wani yunƙuri na karɓar bashi, ko daga cikin gida ko na ƙasashen waje, sai ya bi ta Sashen Kula da Basussuka na Jiha don tantancewa da bin hanyoyin gaskiya,” inji shi.
A nata jawabin, Darakta Janar na PEBEC, Hajiya Zahrah Mustapha Audu, ta yaba wa gwamnatin jihar bisa sauye-sauyen da take aiwatarwa, tana mai cewa taron an shirya shi ne domin kara wayar da kai ga al’umma, karfafa hadin gwiwa da masu ruwa da tsaki, da kuma kara zage damtse wajen sauya fasalin shugabanci da kasuwanci a Jihar Yobe.
Biyan wannan kaso mai tsoka na bashi da gwamnatin Buni ta yi ana kallon sa a matsayin wata babbar nasara wacce za ta taimaka wajen sake farfado da tattalin arzikin jihar da kuma jawo hannun jari mai dorewa.









