Gwamnan Yobe ya fi kowane Gwamna kula da harkar kiwon lafiya a jiharsa – Jaridar Blueprint

0
169
Gwamnan Yobe ya fi kowane Gwamna kula da harkar kiwon lafiya a jiharsa - Jaridar Blueprint

Gwamnan Yobe ya fi kowane Gwamna kula da harkar kiwon lafiya a jiharsa – Jaridar Blueprint

Daga Ibraheem El-Tafseer

Jaridar Blueprint ta zaɓi Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni a matsayin gwarzon gwamna kan harkar kiwon lafiya na wannan shekara, sakamakon irin nasarorin da gwamnatin Buni ta samu a fannin kiwon lafiya.

Manajan Darakta na jaridar Blueprint, Malam Salisu Umar ne ya bayyana haka a yau Talata lokacin da ya ke miƙa wa Gwamna Buni takardar lambar yabo da karramawa.

“Sauyin da aka samu a fannin kiwon lafiya a jihar Yobe abin burgewa ne kuma ya cancanci a ba shi lambar yabo”

“An yi niyya ne don zaburar da mai girma gwamna don ci gaba da yi wa jama’ar ku hidima tare da ƙwazon da aka samu a fannin lafiya,” inji shi.

Gwamna Buni ya yabawa jaridar bisa yadda ta amince da nasarorin da aka samu a jihar musamman a fannin kiwon lafiya.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Yobe za ta mayar da kwale-kwalen Dufuna mai shekaru 8,000 zuwa cibiyar yawon buɗe ido

“Na yi farin ciki da ku da kanku a wurin, kuma abin da kuka gani ya zama labarin abin da kuka gani kuma ku ka shaid da idonku,” in ji shi.

“Mun kafa cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko guda 140, mun inganta cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko guda shida zuwa manyan asibitoci, manyan asibitoci huɗu zuwa asibitocin ƙwararru, mun gyara asibitin koyarwa da na’urorin zamani, sannan muka kafa cibiyar kula da mata da yara mafi girma a Najeriya duk a wani yunƙuri na kawo kiwon lafiya a ƙofar shiga jama’a.” Inji shi.

Gwamna Buni ya sadaukar da wannan karramawar ne ga al’ummar jihar Yobe da suka zuba masa aikinsu, da ma’aikatan da suka yi iya ƙoƙarinsu wajen yi wa jama’a hidima.

“Ina so in tabbatar muku da cewa wannan lambar yabo za ta ƙara zaburar da mu wajen yi wa jama’armu hidima sosai,” in ji shi.

Gwamnan ya yi ƙira ga kafafen yaɗa labarai da su ba da kulawa daidai gwargwado ga ci gaban jihar da ƙasa baki ɗaya.

“Kazalika, ya kamata ku kalli ɓangarorin labaran da ke fitowa daga jihohinmu da ƙasarmu masu kyau, ka da ku wuce gona da iri kan abubuwan da ba su dace ba.

“Wasu daga cikin rahotannin ba a taɓa tantance su ba, wasu kuma abubuwan da suka faru a baya waɗanda ba labari ba ne, illa dai suna yin tasiri ga ci gaban tattalin arziƙi da ci gaban ƙasa,” Buni ya jaddada.

“Dukkanmu muna da nauyin da ya rataya a wuyanmu na gina al’ummarmu, da ƙarfafa juriya da zaburar da shugabanni don samar da kyakkyawan shugabanci,” inji shi.

Leave a Reply