Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP, ya ce fursunoni 38 ne suka tsere daga wani gidan yari mai cunkoso a Moroni, babban birnin ƙasar, bayan da wani soja da aka tsare ya fasa gidan yarin.
Fursunoni da dama sun tsere daga gidan yarin ƙasar Comoros da ba shi da tsaro na kirki ta babbar kofar shiga.
Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP, ya ce fursunoni 38 ne suka tsere daga wani gidan yari mai cunkoso a Moroni, babban birnin ƙasar, bayan da wani soja da aka tsare ya fasa gidan yarin.
KU KUMA KARANTA:Sababbin ’yan haya sun tsere da ’ya’yan maƙwabta 4
Masu gabatar da ƙara sun ce fursunonin sun yi amfani da rashin tsaro mara inganci ne sannan suka fita ta babbar ƙofa. Babu wanda ya jikkata a lamarin.
Sun ce akwai yiyuwar wani soja ne ya shirya fasa gidan yarin, wanda aka kama shi kan mutuwar wani mai sha’awar ƙwallon ƙafa da jami’an tsaro suka bindige yayin da suke ƙoƙarin tare magoya bayan masu ƙwallon, kafin wasan shiga gasar cin kofin duniya a bara.
Sojan na cikin waɗanda suka tsere, sai dai kawo yanzu ba a kama ko ɗaya daga cikinsu ba.