Fitaccen ɗan kasuwa a Najeriya Alhaji Aminu Ɗantata ya rasu
Daga Ibraheem El-Tafseer
Allah Ya yiwa fitaccen ɗan kasuwar Najeriya dake birnin Kano Alhaji Aminu Ɗantata rasuwa a daren ranar Juma’a.
Ya rasu ya na da shekaru 94 da haihuwa a duniya.
An haifi Marigayi Alhaji Aminu Ɗantata a ranar 19 Mayu na shekarar 1931 ya kuma koma ga Allah a ranar 28 ga watan Yuni na shekarar 2025.
KU KUMA KARANTA:Wakiliyar BBC Hausa Bilkisu Babangida ta rasu
Har zuwa yanzu ba a sanar da lokacin jana’izarsa ba a hukumance.
Ya koma ga Allah yana da ‘ya’ya 7 da jikoki da dama ,daga cikin ‘ya’yansa akwai Alhaji Tajuddeen Aminu Dantata sai kuma ɗan ‘yar uwarsa fitaccen attijirin Afrika Alhaji Aliko Ɗangote.
Allah Ya gafarta masa da rahama.









