Wakiliyar BBC Hausa Bilkisu Babangida ta rasu
Daga Jameel Lawan Yakasai
Bilkisu Babangida ta rasu a yau Talata da safe a Abuja bayan doguwar jinya.
Ta rasu tana da shekaru 56 a duniya, ta bar ƴaƴa biyu da jikoki shida.
Kafin BBC, ta yi aiki da gidan radio Kano, gidan radio tarayya FRCN da sashen Hausa na gidan radion Amurka VOA.
KU KUMA KARANTA: Tsohuwar Editar Neptune Prime Amina Alhassan ta rasu
Za a yi jana’izarta yau a babban masallacin Abuja da ƙarfe ɗaya da rabi na rana.
Allah Ya gafarta mata, Ya sanya ta a Aljannah.