No menu items!

Sample Page Title

Date:

EFCC a Kano ta tsare mutane biyu bisa samun su da kuɗaɗen kasashen waje

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Hukumar EFFC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ta ce ta fara bincike kan wasu dubun dubatar kuɗaɗen ƙasar waje da aka kama a filin jirgin sama na Kano.

EFCC ta ce an ga dala 86,500,305 da kuma riyal 305,150 ne cikin wata jaka lokacin da aka ga wani ma’aikacin filin jirgin mai suna Sale Bala ya yi yunƙurin ɗaukar ta ranar Lahadi.

“Bayan bincike, jami’an kwastam sun gano kuɗaɗen ne da aka ɓoye cikin zannunwan gado,” in ji EFCC cikin wata sanarwa.

KU KUMA KARANTA:Matsalar tsaro na ƙara taɓarɓarewa a Najeriya – Amnesty

“An kama Sale Bala da wani Abdullahi Tahir da ake zargin shi ne aka tsara zai karɓi jakar bayan kammala tantance ta.”

Ta ƙara da cewa kuɗin da kuma waɗanda ake zargi na tsare a hannunta, kuma za ta kai su kotu da zarar an kammala bincike.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...