Kakakin Majalisar wakilaiya samo tallafi Naira biliyan 5 don ayyuka a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya
Daga Idris Umar, Zariya
Kakakin Majalisar Wakilai ta Tarayya, Dakta Tajuddeen Abbas, ya samu nasarar samo tallafin naira biliyan biyar (Biliyan 5) daga gwamnatin tarayya domin aiwatar da muhimman ayyukan ci gaba a Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zariya.
Shugaban Karamar Hukumar Zariya, Injiniya Jameel Ahmad Muhammad, ne ya bayyana hakan yayin wata ziyarar ban girma da ya kai wa Shugaban Jami’ar mai barin gado, Farfesa Kabiru Bala.
A cewar Injiniya Jameel, Kakakin Majalisar ya rigaya ya kawo wasu manyan ayyuka a Kongo Campus, ciki har da shigar da hasken wutar lantarki ta hanyar solar mini grid da kuma gyaran filin motsa jiki na Kongo. Ya ce yanzu an fadada ayyukan zuwa Samaru Campus, inda za a gina sabon ginin Sashen Kimiyyar Zamantakewa (Faculty of Social Sciences), da wasu gine-gine bisa bukatar jami’ar.
KU KUMA KARANTA: Matsalar Ruwan Sha: Matasan Geidam sun yaba wa Kashim Musa Tumsah
Farfesa Kabiru Bala, yayin da yake mayar da martani, ya yaba da wannan kokari da Kakakin Majalisar ya yi, yana mai cewa Sashen Kimiyyar Zamantakewa ba ya cikin tsarin farko na ABU, kasancewar ya samo asali ne daga rabe-raben da aka yi a tsohon Sashen Fasaha da Zamantakewa.
Shugaban Jami’ar ya ja hankalin kamfanin da ke aiwatar da ayyukan, Laralec Ultimate Limited, da su tabbatar da inganci. Ya ce jami’ar ba za ta karbi wani aiki da bai da kima ba, kuma inganci yafi kyau fiye da kawata gine-gine kawai.
Farfesa Bala ya gode wa Kakakin Majalisar da Shugaban Karamar Hukumar bisa irin wannan gudunmawa, tare da yin kira ga tsofaffin daliban jami’ar da su ci gaba da tallafa wa alma mater dinsu.
Taron ya samu halartar manyan jami’an jami’ar, ciki har da Mataimakan Shugaban Jami’a — Farfesa Ahmed Doko Ibrahim (Harkokin Gudanarwa), Farfesa Raymond Bako (Harkokin Karatu), da wakilan Sakataren Jami’a, Dr. Aliyu Dalha Kankia; Ma’aji, Malam Garba Shehu; da Mataimakin Musamman ga Shugaban Jami’a, Malam Auwal Yusuf Mohammed Yusuf, da wasu.