Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.
KUNGIYAR iyaye da malaman makaranta (PTA) ta kasa a tarayyar Najeriya ta bayyana rashin jin dadinsu da matakin da kungiyar malaman Jami’a (ASUU) suka dauka na karin lokacin yajin aikin da suka kwashe wata daya su na yi kuma yanzu suka kara tsawaitawa da watanni biyu.
Alhaji Haruna Danjuma, shugaban kungiyar na kasa ne ya bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da manema labarai a game da matakin da kungiyar malaman Jami’a (ASSU) suka dauka na karin watanni biyu domin ci gaba da yajin aikin.
Haruna Danjuma ya ci gaba da cewa sakamakon tattaunawar da aka yi a jiya Lahadi tsakanin bangaren Gwamnatin tarayya da kungiyar malaman Jami’ar ya nuna cewa yan makaranta za su yi wadansu karin watanni biyu kenan in an hada da wata daya da suka kwashe dalibai za su yi watanni uku kenan a gida ba tare da zuwa makarantu ba, lamarin da ya bayyana da cewa ba dadi ko kadan.
Saboda haka “mu iyayen yara muke yin kira ga malaman Jami’a da su koma domin sake duba matakin da suka dauka lallai ba zai haifarwa kowa ‘da idanu mai kyau ba, kuma muna yin kira ga Gwamnatin tarayya da su sani cewa su fa wakilai ne da aka sanya su domin yi wa Jama’a aiki, don haka su yi maza maza su gaggauta domin ganin ba a sake tsawaita lokacin ba na yajin aikin nan, domin lamarin zai iya kawo koma baya ga ilimin Ya’yan mu da kuma Jefa su a cikin wani garari daban don haka ba zai yi mana dadi ba, ba kuma zai yi wa kasa dadi ba.”
Ya ci gaba da cewa ya dace fa idan akwai manyan ma’aikatan Gwamnati da ke iya daukar yayansu zuwa kasashen waje su yi karatu, ai da akwai yan uwan da ba za su iya kai yayansu karatu kasashen waje ba ko makarantun kudi a ciki da wajen Najeriya.
Kuma kashi Casa’in cikin dari na yayan malaman Jami’a duk suna karatu ne a cikin makarantun Najeriya kuma kashi Tamanin cikin dari na manyan ma’aikatan da suke a cikin Najeriya su na da yan Uwa da yayansu ke karatu a Najeriya don haka babu wata hikima a barin yaya ba zuwa makaranta.
“Bangaren shari’a, majalisa duk suna da yaya an koro su daga makaranta don haka muke yin kira ga bangarorin baki daya da su zauna su shawo kan wannan lamari na yajin aikin nan, domin ba zai kawo ci gaba ba saboda haka mu a matsayin iyaye da malaman makaranta muke kara yin roko a duba sosai a shawo kan matsalar.