Connect with us

Siyasa

Atiku ya lashe zaɓe a mazaɓar elRufa’i da ta Ahmed Lawan

Published

on

Atiku Abubakar, ya yi nasara a ɗaya daga cikin rumfunan zaɓe da ke cikin gidan gwamnatin jihar Kaduna. Atiku ya kayar da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Tinubu, a mazaɓa ta 013.

Sakamakon da shugaban jam’iyyar, Kalu kelechi Micheal ya sanya wa hannu, ya nuna cewa APC ta samu 40, jam’iyyar Labour ta samu 48, PDP 69, yayin da NNPP ke da 11.

Wani abin lura shine, Gwamna Nasir El-Rufai na Kaduna, yana ɗaya daga cikin manyan jigajigan yaƙin neman zaɓen Tinubu.

Har ila yau, sakamakon zaɓen shugaban ƙasa, a rumfar da Sanata Ahmed Lawan, shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, ya jefa ƙuri’arsa, ya nuna jam’iyyar PDP tare da ɗan takararta na shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar ya doke abokin takarar sa a jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, da tazara mai yawa.

Rumfar zaɓen, wadda take a makarantar Firamaren Katuzu mai lamba 001B, inda sakamakon ya nuna dan takarar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na APC ya samu kuri’u 107, yayin da Sanata Rabi’u Kwankwaso na NNPC ya samu ƙuri’u 41, sai Alhaji Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP mai ƙuri’u 186.

Sakamakon Majalisar Dattawa a rumfar (001B) ya nuna jam’iyyar APC ta samu yawan ƙuri’u 301, jam’iyyar PDP 37 sai na jam’iyyar NNPP ƙuri’u biyu (2) kacal.

Haka zalika, ɗan takarar kujerar Majalisar Wakilai, a rumfar zaɓen, jam’iyyar PDP ce ta lashe zaɓen da yawan kuri’u 219 fiye da na jam’iyyar APC mai ƙuri’u114.

A daya ɓangaren kuma, a ɗaya rumfar zaɓen (001N-Z), a cikin makarantar Firamaren Katuzu, sakamakon shugaban ƙasa ya nuna PDP ce a kan gaba da ƙuri’u 84, fiye da APC mai ƙuri’u 52, sai NNPP mai 25.

KU KUMA KARANTA:Jama’a sun jikkata biyo bayan hari ranar zaɓe, a Borno

Yayin da APC ta samu ƙuri’u 155, PDP 15 a takarar kujerar Sanatan Arewacin Yobe.Har wala yau, a takarar Majalisar Wakilai, jam’iyyar PDP ta samu kuri’u 103, yayin da APC ta samu 58, NNPC kuma 5.

Har wala yau, a rumfa mai lamba 001A a cikin makarantar Firamaren Katuzu, dan takarar shugaban ƙasa, tare da jam’iyyar sa sun samu kuri’u 113, APC 94, NNPC 26, inda ɗan takarar LP ya samu kuri’u 1 kacalHaka kuma jam’iyyar APC ta samu ƙuri’u 207, PDP 24, NNPC 7 a wannan rumfar (001A) a takarar Sanatan Arewacin Yobe.

Inda kuma PDP ta samu kuri’u 134, APC 89 a takarar Majalisar Wakilai a wannan rumfar.

3 Comments

3 Comments

  1. Pingback: Zaɓen 2023: A daina yaɗa sakamakon zaɓe na ƙarya, in ji ‘yan sanda | Neptune Prime Hausa

  2. Pingback: Yadda Sumaila na NNPP ya kawo ƙarshen Kabiru Gaya na APC da ya shafe shekaru 16 a majalisar dattawa | Neptune Prime Hausa

  3. Pingback: Atiku ya doke Tinubu a Katsina, jihar Buhari | Neptune Prime Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Siyasa

APC ta dakatar da ɗan Majalisa kan cin amana a Zamfara

Published

on

APC ta dakatar da ɗan Majalisa kan cin amana a Zamfara

Jam’iyyar APC reshen Jihar Zamfara ta dakatar da Ɗan Majalisar Wakilai, Aminu Jaji bisa wasu zarge-zargen da ake yi masa na cin amanar jam’iyyar.

Sakataren Yaɗa Labarai na Jam’iyyar APC na Jihar, Malam Yusuf Idris ne ya sanar da dakatarwar a wani taron manema labarai a Gusau a ranar Juma’a.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, Jaji yana wakiltar mazaɓar Ƙaura-Namoda/Birnin-Magaji a Majalisar Wakilai a ƙarƙashin jam’iyyar APC.

Idris ya ce wasu zarge-zargen da ake yi wa Ɗan Majalisar sun haɗa da aikata rashin gaskiya da rashin zuwa tarurrukan jam’iyyar da kuma sauran ayyuka.

KU KUMA KARANTA: Kotun Najeriya ta bayar da umarnin dakatar da asusun banki fiye da dubu 1

Ya ce, matakin ya biyo bayan sanarwar dakatarwar da aka yi wa Jaji daga shugabannin jam’iyyar APC na mazaɓar Birnin-Magaji bisa zargin cin amanar jam’iyyar da dai sauran abubuwan da suka saɓa wa jam’iyyar.
Idris ya ce, “Kwamitin zartaswa na jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Birnin Magaji ne ya miƙa sanarwar dakatarwar zuwa hedikwatar jam’iyyar APC ta jihar.

Bayanai sun ce kwamitin zartaswar jam’iyyar APC na jihar ya gudanar da taron gaggawa a sakatariyar jam’iyyar da ke Gusau a ranar Juma’a 17 ga watan Mayu, 2024, inda aka gabatar da batun dakatar da Jaji ga ‘yan majalisar zartarwar jihar.

Continue Reading

Labarai

Tsohon gwamnan Katsina, Shema ya sauya sheƙa zuwa APC

Published

on

Tsohon gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Shema, a hukumance ya koma jam’iyyar APC Mai mulki a jihar.

Shema, ya kasance gwamnan jihar a tsakanin shekarar 2007 zuwa 2015, a ƙarƙashin jam’iyyar PDP.

Tsohon gwamnan ya yi rajista ne a ofishin jam’iyyar na mazaɓar Shema, ƙaramar hukumar Dutsin-ma, inda shugaban jam’iyyar na jihar, Sani Aliyu-Daura ya ba shi katin zama ɗan jam’iyyar APC.

Lambar katin Shema ta zama ɗan jam’iyyar ita ce: 26551.

KU KUMA KARANTA:Gwamnatin Yobe za ta mayar da kwale-kwalen Dufuna mai shekaru 8,000 zuwa cibiyar yawon buɗe ido

Malam Aliyu-Daura ya yabawa Gwamna Dikko Raɗɗa da kuma tsohon gwamnan jihar Aminu Masari wanda ya gada, a bisa rawar da suka taka wajen ganin Shema ya sauya sheƙa.

Don haka ya tabbatar wa tsohon gwamnan cewa za a yi masa adalci kamar kowane ɗan jam’iyya.

Shugaban ma’aikata na Raɗɗa, Jabiru Abdullahi-Tasuri, shi ne ya miƙa katin zama ɗan jam’iyya ga Shema a madadin gwamnan a jiya Alhamis a Dutsin-ma.

Continue Reading

Labarai

Fusatattun matasa sun lakaɗawa kwamishina duka a wajen zaɓen fidda gwani

Published

on

Banji Ajaka, kwamishinan lafiya na jihar Ondo, ya gamu da fushin matasa a jiya Asabar yayin da ake gudanar da zaɓen fidda gwani na gwamna na jam’iyyar APC mai mulki a jihar.

Daily Trust ta gano cewa Dakta Ajaka, wanda ke Mazaɓar Ugbo 3, a ƙaramar hukumar, ana zarginsa da ɓoye takardar sakamakon zaɓen.

Shaidu sun tabbatar da faruwar lamarin a wata tattaunawa da suka yi da manema labarai, inda suka yi zargin cewa fusatattaun matasan ‘ya’yan jam’iyyar APC ne da ke adawa da tsarin da aka bi wajen gudanar da zaɓen.

Ɗaya daga cikin waɗanda suka shaida lamarin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa rikicin ya faro ne lokacin da ‘yan ɗaya ɓangaren na jam’iyyar suka buƙaci ganin takardar sakamakon zaɓen na fidda gwani.

KU KUMA KARANTA:An yi jana’izar tsohon gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu

“Sun fusata ne suka buƙaci jami’in zaɓe ya ba su takardar sakamakon zaɓen sai kuwa ya ce ta na wajen Ajaka.

“Don haka suka yi masa duka a wurin, inda kuma garinsu ne. Jama’a sun fusata sosai da lamarin, inda rigimar ta ƙare a wajen.”

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Dakta Ajaka ya ce an zarge shi ne da riƙe takardar sakamakon zaɓen.

Ya yi bayanin cewa a lokacin da yake ƙoƙarin bayyana kansa, ’yan daban sun auka masa inda suka yi masa mugun duka.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like