An tono kuɗi a gidan wani jami’in Kwastam da ya rasu

0
453
An tono kuɗi a gidan wani jami'in Kwastam da ya rasu
Yadda takardar kuɗin ta ruɓe

An tono kuɗi a gidan wani jami’in Kwastam da ya rasu

Daga Ibraheem El-Tafseer 

An gano takardun kuɗi na ƙasashen waje da na gida da suka haɗa da Naira, Fam na Birtaniya, da Dalar Amurka da ake zargin an binne su a cikin gidan wani tsohon jami’in kwastam da ya rasu, wanda ke zaune a cikin unguwar kwastam da ke gaban Kwalejin Ilimi ta Tarayya (FCE) Kano.

Rahotanni sun bayyana cewa kafin rasuwarsa, mamacin ya binne kuɗaɗen a cikin gidan ba tare da sanar da ko ɗaya daga cikin ‘ya’yansa ba. Sai dai shekaru bayan rasuwarsa, yayin da ake gyaran wani ɓangare na ƙofar gidan a shekaranjiya, an ci karo da jakunkuna cike da kuɗaɗen da ke da nau’o’i da sikelin ƙasashe daban-daban.

KU KUMA KARANTA: Wani mutum ya kashe ɗan uwansa a dalilin naira 1500 kudin wutar lantarki, a jihar Anambra

Hoto da aka dauka daga wurin ya nuna yadda kuɗaɗen suka lalace sakamakon dadewa da suka yi a ƙasa.

Al’umma sun bayyana mamakinsu tare da tambayar yadda har irin wannan adadi na kudi zai ɓoye ba tare da wani ya sani ba har zuwa rasuwar mamacin.

Leave a Reply