Gwamnatin Kano ta dakatar da shigo da kayan Gwangwan daga Arewa maso Gabas
Daga Jameel Lawan Yakasai
Gwamnatin Jihar Kano ta umarci masu sana’ar gwangwan su dakatar da shigo da kayayyakin gwangwan daga yankin Arewa maso Gabas.
Kwamishinan Tsaro na jihar Kano, AVM Ibrahim Umaru (mai ritaya), ya bayyana hakan a Larabar nan.
KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Kano ta ba da umarnin farfaɗo da makarantar Faransanci da Sinanci a jihar
Kwamishinan ya ce wannan mataki ya biyo bayan iftila’in fashewar bama-bamai da aka samu a kwanakin baya.
Ya ce, bincike ya nuna cewa bama-baman da suka tashi an shigo da su ne daga a kayan gwangwan daga yankin Arewa maso gabas inda aka samu rikice-rikicen Boko Haram.