An kwantar da Tsohon Shugaban Kasa Buhari a ICU a Landan
Daga Jameel Lawan Yakasai
Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na fama da rashin lafiya, kuma rahotanni sun ce kwanan nan aka sallame shi daga dakin kula da masu matsananciyar rashin lafiya (ICU) a wani asibiti da ke Landan a kasar Birtaniya.
Wani makusancin tsohon shugaban ya bayyana cewa Buhari ya kamu da rashin lafiya ne a Landan yayin da ya je don duba lafiyarsa.
Rahoton ya ce an kwantar da Buhari a dakin ICU, amma daga bisani aka sallame shi makon da ya gabata.
Ko da ya ke ba a bayyana irin cutar da ke damunsa ba, rahotanni sun nuna cewa yana samun sauki a Landan, kuma ana sa ran zai dawo Najeriya da zarar ya warke gaba ɗaya.
KU KUMA KARANTA:Ba zan taɓa juyawa APC baya ba – Buhari
Bisa bayanan daga wasu majiyoyi masu tushe, Mamman Daura – kawun Buhari kuma amintaccensa – shima yana samun sauki daga rashin lafiya a kasar Birtaniya.
Buhari bai halarci bikin cika shekaru 50 da kafuwar Kungiyar raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afrika (ECOWAS) da aka gudanar a Legas ranar 28 ga Mayu ba.
A wata wasika da ya aika wa Shugaba Bola Tinubu, Buhari ya bayyana cewa rashin halartar sa taron ya samo asali ne daga tafiyarsa ta duba lafiya a Birtaniya.