No menu items!

Sample Page Title

Date:

Wannan mutumin mai suna Dakta Noah Kekere (likitan bogi) shi ne mai Asibitin “Murna Clinic and Maternity dake Jos sannan kuma fasto ne.

Wannan matar mai suna Misis Busari Kehinde taje asibitin a yi mata tiyata na cire appendix. Ashe shi wannan mutumin ya cire mata ƙoda (kidney) guda ɗaya domin sayarwa ba tare da ta sani ba.

KU KUMA KARANTA: Cin zarafi ne, canza wa yara halittar fata – Likitan fata

Bayan an gama aikin ne da kwanaki take ta jin raɗaɗin ciwo a ciki sai ta tafi babban asibitin koyarwa na Jos (University of Jos Teaching Hospital). Nan ne fa aka gano ai ƙoda ɗaya take da shi maimakon biyu kuma ba a daɗe da cire ɗayar ba.

Ya amsa laifin shi sai dai yanzu yana ƙoƙarin iƙirarin cewa shi mahaukaci ne, yana da matsalar ƙwaƙwalwa.Abin da nake so jama’a su sani shi ne, Dakta Noah Kekere ba likita bane, hasali ma ilimin tattalin arziki (economics) ya karanta, sai kuma wata school of health da ya je.

Jama’a a kiyaye zuwa asibitin da ba su da lasisi da shaidar rijista daga gwamnati. A yi hankali a kula sosai, domin akwai ma’aikatan bogi (quacks) da dama.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...