An sace limaman coci 6 a Anambara

0
101

Rahotanni daga Najeriya na cewa ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu limaman Coci shida yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa birnin Awka na jihar Anambara a kudu maso gabashin Najeriya.

Bayanai sun yi nuni da cewa ‘yan bindigar sun sace Archbishop Uka Uka na Mujami’ar Brotherhood of the Cross and Star, (BCS) da matarsa Anne Osim da ɗansu Ronald Uka Osim.

Sauran limaman Cocin sun haɗa da Azuka Ochu, Moses Okafor da Anderson Akwazie a cewar jaridar Daily Trust.

Jaridar Daily Post ta yanar gizo ta ruwaito cewa mutanen na hanyarsu ta zuwa Awka ne daga jihar Abiya don gudanar da ayyukan wa’azi a lokacin da lamarin ya faru.

Al’amarin ya faru ne a ranar 1 ga watan nan na Mayu kamar yadda rahotanni suka nuna.

KU KUMA KARANTA:An halaka direba da sace mutum 2 a hanyar Abuja

“Mun damu matuƙa, amma muna da tabbacin cewa Ubangijin da suke bautawa zai taimaka musu.” Jaridar ta Daily Post ta ruwaito wani Limami a Cocin ta BCS, Bishop Denis Onuoha yana cewa.

Sai dai rundunar ‘yan sandan jihar Anambara, ta ce ba ta da masaniyar aukuwar wannan al’amari.

“Ba mu da wasu bayanai da suka nuna aukuwar wannan al’amari a jihar Anambara.” Wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na Facebook ta ce a ranar Asabar ɗauke da sa hannun Kakakinta SP Tochukwu Ikenga.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “muna ƙira ga jama’a da su taimaka mana da bayanai kan wannan al’amari idan har ya faru, hakan zai ba mu dama mu ƙaddamar da bincike.”

Leave a Reply