An kama sojojin Najeriya kan zargin sata a matatar mai ta Ɗangote

0
117

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta damu matuƙa kan zargin da ake yi wa wasu jami’anta biyu da yin sata a Matatar Mai ta Aliko Ɗangote da ke Legas.

“Wannan aika-aika, wadda dakarun sa-kai da jami’an tsaro masu zaman kansu da ke aiki a matatar man suka daƙile, abu ne da ba za a amince da shi ba, kuma abin takaici ne matuƙa. Don haka ba ya wakiltar ɗa’a da ƙimar rundunar soji,” in ji sanarwar da rundunar ta wallafa a shafinta na X a ranar Laraba.

Ta ce tuni aka gano waɗanda ake zargin kuma ana tsare da su a yanzu haka.

“Binciken farko ya bayyana cewa wani ɗan kwangila ne da aka bayyana sunansa da Mista Smart ya ɗauki hayar mutanen biyu, wanda ya yi ikirarin cewa yana so ne ya ƙwato wasu igiyoyin sulke na da ya bari a harabar matatar.

KU KUMA KARANTA: Ɗangote ya karya farashin dizel zuwa N1,000 kan kowace lita

“Su sojoji ba su sani ba,da ɗan kwangilar ya gano za a samu matsala a lokacin da suke tunkrara wajen bincike na matatar, sai ya ɗauki uzuri ya fice daga motar ya bar su a wajen,” a cewar sanarwar.

Rundunar ta ce ana ci gaba da bincike don gano da tabbatar da cikakken laifin sojojin da aka kama.

Kazalika ta ce an gano wayoyin da aka sace ɗin kuma ƙwace su.

Rundunar soji ta ce tana aiki ƙut da ƙut da hukumar gudanarwar Matatar Mai ta Dangote don tabbatar da cewa an yi cikakken bincike a kan “wannan mummunan lamari.”

“Rundunar soji na son tabbatar wa da jama’a cewa za a dauki matakan ladabtarwa da suka dace kan wadanda suka aikata laifin, saboda ba za ta lamunci irin wannan wani laifi a cikin ma’aikatanta ba,” ta ƙara da cewa.

Leave a Reply