Amurka ta ja hankalin ‘yan siyasar Isra’ila da su kiyayi rura wutar rikici tsakanin su da Falasɗinu

0
23
Amurka ta ja hankalin 'yan siyasar Isra’ila da su kiyayi rura wutar rikici tsakanin su da Falasɗinu

Amurka ta ja hankalin ‘yan siyasar Isra’ila da su kiyayi rura wutar rikici tsakanin su da Falasɗinu

A ranar Alhamis ɗin nan Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ziyarci dakarun Isra’ilan a kudancin Gaza, a yayin da tankokin yaƙin Isra’ilan ke ƙara nausawa cikin Rafah. Ziyarar ta shi ta zo ne a lokacin da Netanyahu ke shirin gabatar da jawabi gaban Majalisar dokokin Amurka a Washington, cikin mako mai zuwa.

Ziyarar da ta ba da mamaki ta zo ne bayan da ministan tsaron ƙasa na Isra’ila Itamar Ben-Gvir ya ziyarci wani wurin ibada da ake jayayya a kan shi dake birnin kudus a rana guda.

KU KUMA KARANTA:Biden ya yi alƙawarin kare Isra’ila daga harin ramuwar gayya na Iran

Ofishin Netanyahu ya sanar da batun kai ziyarar bayan ya bar kudancin Gaza, inda daga bisani ya fitar da sanarwar da ta ce ‘’jajircewar da sojoji su ka yi ne ya taimaka mana samun ci gaba kan yarjejeniyar sakin waɗanda aka yi garkuwa da su.’’

Tun da farko, Majalisar dokokin Isra’ila, cikin sauƙi ta zartar da kudurin dokar da ya yi adawa da kafa ƙasar Falasɗinu.

Mai Magana da yawun Majalisar tsaron ƙasa na Amurka, John Kirby, yace, bai kamata yan siyasar Isra’ila su ruruta wutar fitina ba, ta ziyar da Be-Gvir ya kai zuwa masallacin Al-Aqsa.

Kirby ya ƙara da cewa, ‘’zamu ci gaba da jan hankalin abokan hulɗar mu a Izra’ila da kar su yi wani abun da zai rura wutar dake ci a yanzu, ko wani abu da ka iya mara bayan tashin hankali ta ko wacce hanya.’’

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here