Binciken masana ya tabbatar da cewar itacen bagaruwa na da matukar amfani sosai tun jikin ɗan Adam kama daga ganye, itace da kuma ‘ya’yanta.
Noman itacen Bagaruwa ya fi yawa a busassun wuraren sannan ƙasar Australia da ƙasashen Larabawa na cikin kasashen da suka fi nomanta.
Ga amfanin da yake yi a jikin mutum:
- Bagaruwa na maganin tsutsar ciki.
- Itacen bagaruwa na maganin gudawa mai tsanani.
- Yana kuma kawar da matsalar zubar jini.
- Bagaruwa na maganin ciwon hakori: Ana daka ‘ya’yan Bagaruwa a riga zubawa ko kuma a samu ‘ya ‘yan ta wayanda basu bushe ba a riqa matsa ruwanta a cikin wurin.
- Bagaruwa na maganin ciwon sikari wato ‘Diabetes’.
- Bagaruwa na kawar da warin jiki da warin baki.
- Yana magani da hana kamuwa da cutar sanyi musamman a jikin mata.
- A samu ganyen Bagaruwa a tafasa idan ya tafasu a juye a buta a riga wanke idanu da shi duk safiya wannan yana kawar da jan ido da kuma yanar ido.
- Yana kara karfin mazakuta.
- Bagaruwa na maganin cutar Hepatitis C.