Abubuwan da ya kamata musulmi ya yi don samun falala a kwanaki 10 na Dhul-Hijja
Daga Shafaatu Dauda Kano
Alhamdulillah, tsira da aminci su tabbata ga Annabi Muhammad (SAW), jagoran al’umma da mafi girman annabawa.
Kwanaki goma na watan Dhul-Hijja na daga cikin lokuta mafi girma da Allah ya tsara domin bauta da ayyukan alheri. Annabi Muhammad (SAW) ya tabbatar mana cewa wadannan kwanaki sun fi kowanne lokaci daraja da lada a idon Allah.
Me ya sa kwanaki goma na Dhul-Hijja suka fi muhimmanci?
Annabi (SAW) ya ce, babu wani aiki na ibada da zai kawo lada kamar wanda ake yi a cikin kwanaki goma na Dhul-Hijja. Saboda haka, wajibi ne mu himmatu wajen yin ayyukan alheri da ibada cikin tsantsar niyya da tsarkin zuciya.
KU KUMA KARANTA: Hukumar Hisbah a Kano ta kama matasan da ba sa yin azumi da masu aikin banza
Wadanne ayyuka ya kamata mu mayar da hankali a kansu?
Ga jerin ayyukan ibada da suka dace mu yi cikin wannan lokaci:
1.Tuba da dawowa ga Allah da zuciya daya.
2.Nisantar duk wani zunubi da ke raba mu da rahamar Allah.
3.Zikirin Allah, kamar tasbihi, tahmidi da takbiri.
4.Karatun Al-Qur’ani da tunani a cikin ayoyinsa.
5.Biyayya ga iyaye, malamai da shugabanni.
6.Kyautatawa marayu da masu bukata.
7.Ciyar da talakawa da masu rauni.
8.Ziyarar marasa lafiya.
9.Azumi, sallah da sadaqah.
10.Yanka (layya) da hajji ko umrah ga masu ikon yin hakan.
Yin addu’a da neman kusanci ga Allah.
Muhimman falaloli da lada a cikin kwanaki goma na Dhul-Hijja
Allah ya yi rantsuwa da wadannan kwanaki a cikin Suratul Fajri (89:1-2).
Wadannan kwanaki ana kiransu Ayyamin Ma’alumaat (kwanaki sanannu) saboda girman su.
Ana ninka lada na ayyukan alheri a cikin su.
An karbo daga Annabi (SAW) cewa babu wani lokaci da Allah ke son ayyukan alheri kamar wannan lokaci.
Akwai ranar Arafa, ranar da aka fi samun gafara da ‘yanci daga wuta.
Ranar Sallah Babba, wadda ita ce rana mafi daraja a duniya, tana cikin kwanakin.
Shedan na ta tuzarta saboda yawan bayin Allah da ake ‘yantawa daga azaba a wannan lokaci.
Mu dauki kwanaki goma na Dhul-Hijja a matsayin wata babbar dama ta kusantar Allah ta hanyar ibada da ayyukan alheri. Muna rokon Allah ya amsa mana addu’o’i, ya karbi ayyukanmu, ya gafarta mana, ya kuma bamu ikon bauta masa yadda ya dace.
Amin.









