Kano ta zama cibiyar binciken maganin cututtukan zamani— Farfesa Hamisu Salihu

0
66
Kano ta zama cibiyar binciken maganin cututtukan zamani— Farfesa Hamisu Salihu

Kano ta zama cibiyar binciken maganin cututtukan zamani— Farfesa Hamisu Salihu

Daga Shafaatu Dauda Kano

Darakta Janar na cibiyar bincike mai zaman kanta a jihar Kano (KIRCT), Farfesa Hamisu Salihu, ya bayyana sabbin fasahohin zamani da aka samar a bangaren lafiya sun sanya Jihar ta fara taka rawa a matsayin cibiyar da za ta rinka bayar da kulawa da magani na zamani a Najeriya.

Farfesa Salihu ya bayyana hakan ne a jiya Talata, a yayin wata ziyarar duba wuraren aikin cibiyar da ke Kwanar Dawaki a karamar hukumar Dawakin Kudu, wadda take dauke da na’urori na zamani da ake amfani da su wajen bincike, nazari, gano cututtuka da sauran bangarorin da ke kara haɓɓaka fannin kiwon lafiya.

A cewarsa, “Samar da sabuwar na’urar Next Gen 2000, zai taimaka wa marasa lafiya musamman masu fama da cutar Kansar Mama wajen gano ainihin nau’in cutar da ke damunsu, ta hanyar saukaka samun maganin da ya dace da kowanne nau’i na cutar, da kuma karfafa damar warkar da marasa lafiya”.

KU KUMA KARANTA: Abubuwa 10 da za su iya faruwa idan Tinubu ya zarce a wa’adi na biyu – Hasashen KY Tebo

Ya kara da cewa, tare da na’urori irin su MI SEQ 1100+, B2 Solo – DNA, da kuma fasahar pharmacogenomics, jihar Kano ta yi watsi da tsaffin hanyoyin kula da cututtuka, ta kuma rungumi tsarin binciken ainihin tushen cuta da samar da maganin da ya dace da kowanne mutum.

“Mun fara rage kashe kudade a bangaren lafiya, da kuma kara kudaden shiga ga jihar Kano, tare da inganta tsarin kiwon lafiya a jihar da kuma kasa baki daya”.

Har ila yau, ya bayyana cewa Hukumar Kula da Yaduwar Cututtuka ta Kasa (NCDC) da wasu hukumomin tarayya sun nuna sha’awarsu ga wannan cibiyar, ta yadda suke shirye-shiryen turo ma’aikatansu zuwa Kano domin koyon yadda ake amfani da fasahar genomics surveillance a kasar.

Leave a Reply