A karon farko a tarihi, mace ta zama shugabar ƙaramar hukuma bayan lashe zaɓe a jihar Borno

0
188

Daga Maryam Umar Abdullahi

A karon farko a tarihi, an samu macen da ta zama zabaɓɓiyar shugabar ƙaramar hukuma guda a jihar Borno da ke arewa maso gabas.

Hukumar zaɓe ta ayyana Hajiya Inna Galadima ta jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin wadda ta lashe zaɓen karamar hukumar Jere a Borno, rahoton Daily Trust.

Baturen zaɓen ƙaramar hukumar, Farfesa Mohammed Konto, shi ne ya ayyana Galadima, tsohuwar kwamishina da mai bada shawara a matsayin wacce ta ci zaɓen.

KU KUMA KARANTA: Ya zama dole a amince da haƙƙin Falasɗinawa na kafa ƙasarsu – Majalisar Ɗinkin Duniya

Konto ya ce ƴar takarar APC ta samu kuri’u 110,459 inda ta kayar da babban abokin hamayyarta na Peoples Democratic Party (PDP) wanda ya samu ƙuri’u 2,478.

Ranar Asabar da ta gabata, 20 ga watan Janairu, 2024 aka gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi 27 da kansiloli sama da 300 a jihar Borno wadda APC ke mulki.

Rahoton The Cable ya nuna cewa jam’iyyar APC ta samu nasarar lashe zaɓukan kujerun ciyamomi a sauran kananan hukumomin jihar Borno guda 26, duk da wannan 27 kenan.

Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar (BOSIEC), Alhaji Lawan Maina, shi ne ya sanar da haka a sakamakon da ya bayyana ranar Lahadi a Maiduguri, baban birnin jihar.

A jawabinsa bayan kammala tattara sakamako, Alhaji Maina ya ce:
“All Progressive Congress (APC) ta samu nasarar lashe kujerun ciyamomi 27 da ke faɗin jihar, haka nan kuma ita ta samu nasara a zaɓen kansiloli 312.”

Leave a Reply