SDP ta kori El-Rufai daga jam’iyyar na tsawon shekaru 30

0
160
SDP ta kori El-Rufai daga jam’iyyar na tsawon shekaru 30
Nasiru Elrufai

SDP ta kori El-Rufai daga jam’iyyar na tsawon shekaru 30

Daga Jameel Lawan Yakasai

Jam’iyyar SDP ta kori tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, daga jam’iyyar tare da haramta masa shiga ko hulɗa da jam’iyyar tsawon shekaru 30.

Sanarwar da mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Araba Rufus Aiyenigba, ya fitar a Abuja ta ce El-Rufai ya karya doka ta hanyar bayyana kansa a matsayin ɗan jam’iyya ba tare da ya yi rajista da jam’iyyar ba, tare da amfani da takardun bogi da hotuna da wasu shugabanni da aka dakatar don ƙarfafa ikirarin nasa.

SDP ta zargi El-Rufai da ƙoƙarin tarwatsa jam’iyyar ta hanyar haɗa SDP da wata haɗakar siyasa ba tare da amincewa ba, da kuma ci gaba da yin siyasa da wata jam’iyyar wato African Democratic Congress (ADC) — duk da cewa bai da hurumin hakan.

Jam’iyyar ta ce duk da cewa El-Rufai ya sha alwashin shiga jam’iyyar, bincike ya tabbatar cewa bai yi rajista a mazabarsa ta Unguwar Sarki da ke Kaduna ba, maimakon haka ya ƙirƙiri katin rajista da kansa kuma ya ɗauki lambar mamba ta farko.

KU KUMA KARANTA: Majalisar jihar Kaduna za ta ɗauki mataki kan yaron El-Rufa’i

SDP ta ce El-Rufai ya kasance yana amfani da sunan jam’iyyar wajen gudanar da wasu taruka da hulɗa da wasu mutane da ke ƙoƙarin tada rikici a cikin jam’iyyar.

Jam’iyyar ta bukaci hukumar INEC da sauran hukumomi su ɗauki El-Rufai a matsayin wanda ba ɗan jam’iyya ba ne, tare da jaddada cewa ba ya da hurumin wakiltar jam’iyyar a ko’ina.

Ta kuma jaddada aniyarta ga dimokuraɗiyya, da’a, gaskiya da tsabta a siyasa tare da gayyatar dukkan ‘yan Najeriya da ke da kishin ci gaban ƙasa da su shiga jam’iyyar ta hanyoyi na doka da gaskiya.

Leave a Reply