Gwamnatin Najeriya ta saka tsohon jirgin shugaban ƙasa a kasuwa 

0
323
Gwamnatin Najeriya ta saka tsohon jirgin shugaban ƙasa a kasuwa 
Tsohon jirgin shugaban Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta saka tsohon jirgin shugaban ƙasa a kasuwa

Daga Jameel Lawan Yakasai 

Gwamnatin tarayya ta kammala shirin sayar da jirgin shugaban kasa kirar Boeing Business Jet (737-700 BBJ), a kasar Switzland.

Hakan ya biyo bayan sayan sabon jirgin shugaban kasa kirar Airbus A330, wanda kudinsa ya haura naira biliyan N150bn, a shekarar 2024.

KU KUMA KARANTA: Jirgin Rano Air ya gamu da matsalar inji a sararin samaniya

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ne ya sayo tsohon jirgin a shekarar 2005, wanda aka shafe shekaru 20 ana amfani dashi.

Tsaffin shugabannin Najeriya da suka yi amfani da tsohon jirgin sun hada da Obasanjo, Yar’adua, Jonathan, Buhari da kuma shugaba Tinubu kafin ya sayo sabon jirgi.

Leave a Reply