Jirgin Rano Air ya gamu da matsalar inji a sararin samaniya
Daga Jameel Lawan Yakasai
Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Ƙasa (NCAA) ta dakatar da jirgin Rano Air daga tashi daga Sakkwato zuwa Kano biyo bayan matsalar injin da ta faru lokacin yana sararin samaniya.
Daraktan hulɗa da jama’a da kare hakkin fasinjoji na NCAA, Michael Achimugu, ya ce jirgin Rano Air mai lamba 5N-BZY ya samu matsala a ɗaya daga cikin injinan sa yayin da yake sararin samaniya, amma matukin jirgin ya sauke shi lafiya.
KU KUMA KARANTA:Jirgin ‘Max Air’ ya tunkuyi ƙasa wajen sauƙa a filin jirgin saman Mallam Aminu Kano
Ya bayyana cewa an ga hayaki daga injin jirgin, wanda ya sanya aka gaggauta aiwatar da matakan tsaro, kuma NCAA ta dakatar da jirgin daga sake tashi har sai an kammala bincike.
“Jirgin Rano mai lamba 5N-BZY ya samu matsala a injin na 1. An lura da hayaki a cikin ɗakin fasinja da inda matuki ke zaune. An kunna na’urar lumfashi. An ɗauki dukkan matakan tsaro da suka dace kafin sauka.
” Hayakin daga baya ya gushe. Matukin jirgin ya saukar da jirgin lafiya ba tare da wata matsala ba,” in ji Achimugu a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Litinin.