Ƙungiyar Matasa YSPUF ta karrama mataimakin kwamandan Hizba na shiyyar Yobe ta Kudu (Hotuna)

0
322
Ƙungiyar Matasa YSPUF ta karrama mataimakin kwamandan Hizba na shiyyar Yobe ta Kudu (Hotuna)

Ƙungiyar Matasa YSPUF ta karrama mataimakin kwamandan Hizba na shiyyar Yobe ta Kudu (Hotuna)

Daga Ibraheem El-Tafseer

Ƙungiyar Matasa mai suna Yobe South Progressive Unity Front (YSPUF) ta karrama mataimakin kwamandan Hizba na shiyyar Yobe ta Kudu (Zone B), sannan tsohon shugaban ƙaramar hukumar Potiskum, Hon. Alhaji Muhammad Musa Potiskum.

An gudanar da taron ne ranar Lahadi da ta gabata, babban ɗakin taro na cikin sakatariyar Potiskum.

Shugaban matasan ya bayyana dalilin karramawar da cewa, “mun karrama shi ne saboda irin ƙoƙarin da ya ke a gudanar da ayyukan Hizba a wannan yanki na shiyyar Yobe ta Kudu (Zone B). Sannan mun duba irin ayyukan ci gaba da ya kawo a lokacin da ya ke shugaban ƙaramar hukumar Potiskum, wanda har zuwa yanzu ana morar ayyukansa” inji shi.

KU KUMA KARANTA: Ƴaƴan kungiyar wakilan kafafen yada labarai ta Kano su 15 na tuhumar Shugabannin su da laifin ha’intar su

Jama’a da dama ne suka halarci wajen taron, sun haɗa da, tsohon shugaban ƙaramar hukumar Potiskum, Hon. Alhaji Yusuf Yahaya, Hon. Audu Hussaini, Hon. Barrister Khalil, Sakataren ƙaramar hukumar Potiskum Hon. Bowu, da sauran jiga-jigan dattijai a Siyasar Potiskum, irin su Alhaji Muƙaddas.

Sannan akwai Malaman addini, irin su Shaikh Abdallah Mahmud Adam, Shaikh Mukhtari Waliy Ibn Shaikh Kabir da Malam Buhari.

Tun da farko, sai da aka karanto taƙaitaccen tarihin Alhaji Muhammad Musa Potiskum ɗin, inda aka jero irin karatuttukan da ya yi da kuma gwagwarmayar da ya sha a siyasa tun lokacin NPN. Sannan an karanto irin muƙaman da ya riƙe a matakin aikin gwamnati.

Leave a Reply