Fittaccen jarumin Kannywood Adam A. Zango Yayi Hatsarin mota
Daga Jameel Lawan Yakasai
Hatsarin da ya rutsa da fitaccen jarumin da wasu abokan sana’arsa ya afku ne a Kwanar Dangora Kafin Maiyaki,
Daga nan al’ummar yankin suka yi gaggawar kai shi wani asibiti dake garin Kwankwaso a Karamar hukumar Madobin jihar kano, daga nan ake sa ran wucewa dashi wani babban asibitin kamar yanda daya daga cikin yaransa da suka gamu da hatsarin tare ya sanar da majiyarmu a daren jiya.
KU KUMA KARANTA: Gwamnan Ogun Abiodun ya baiwa iyalan ƴan wasan Kano da su ka rasu a hatsarin mota Naira Miliyan 31
Wakilin Jaridar Neptune Prime ya tuntubi mashiryin shirin wasan kwai-kwai a Kano, Abdul’aziz Dan small, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace yanzu haka Adamu na kwance a wani asibiti yana karbar kulawar likitoci.
Jarumin ya bayyana godiyarsa ga masoyansa a shafinsa na Fesibuk bisa ga addu’o’in da suke masa.
Sannan kuma ya yi kira ga masoyan sa da su kwantar da hankalinsu, domin sauki yana samuwa.