Rundunar Ƴansanda ta Kano ta gano AK-47 ta bogi a gidan daya daga cikin wadanda ake zargi da kisan DPO na Rano

0
389

Daga Jameel Lawan Yakasai

Rundunar ƴansandan Jihar Kano ta ce ta gano wata bindiga mai kama da AK-47 amma ta bogi ce, a gidan ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi da hannu a kisan CSP Baba Ali, wanda ya kasance jami’in ‘yan sanda mai kula da yankin karamar hukumar Rano.

Mai magana da yawun rundunar, SP Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

A cewarsa, an gano bindigar ne yayin wani samame da aka kai gidan ɗaya daga cikin waɗanda aka kama da alaƙa da kisan DPO ɗin.

KU KUMA KARANTA:Kotu a Kano ta tura Mutane 29 da ake zargi da Kashe DPOn Rano gidan Yari

“Lokacin binciken gidan ɗaya daga cikin waɗanda aka kama dangane da zargin kisan DPO na Rano, an gano bindigar AK-47 ta bogi ,” in ji Kiyawa.

CSP Baba Ali ya samu munanan raunuka sakamakon rikicin da ya barke bayan mutuwar wani matashi a hannun jami’an tsaro, kuma ya rasu ne a yayin da ake kokarin ceto ransa a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano.

Leave a Reply