Kotu a Kano ta tura Mutane 29 da ake zargi da Kashe DPOn Rano gidan Yari
Daga Jameel Lawan Yakasai
Kotun Majistare mai lamba 20 da ke Noman’s Land a Kano, ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Fauziyya Isa Sheshe, ta tura mutane 29 gidan yari bisa zargin su da hannu a kisan Baturen ’Yan Sandan Rano, CSP Baba Ali.
Yayin zaman Kotun lauyar gwamnati, Barista Saima Garba, ta karanta musu kunshin tuhumar da ake yi musu.
Ana zargin su da laifukan da suka haɗa da hada baki wajen tayar da fitina, barna, shiga gida ba tare da izini ba, sata da kuma kisan kai, laifukan da suka sabawa sassa da dama na Penal Code, ciki har da sashe na 221.
KU KUMA KARANTA: Rundunar ‘Yan Sanda Kano ta kama manyan waɗanda ake zargi da hannu a kisan gillar DPO din Rano, Marigayi CSP Baba Ali
Daga cikin waɗanda ake zargi har da Yusuf Baba, Bala Muhammad, Abdullahi Salisu Kere, Dadi Buhari, Musa Munkaila da kuma Ladi Ismail, wadda ake zargi da tunzura matasa har suka kona gidajen jama’a a garin Rano.
Kotu ta tura wadanda ake zargin gidan yari har zuwa ranar 16 ga Yunin da mu ke ciki don ci gaba da sauraren shari’ar.
Rahotanni sun kuma nuna cewa akwai kimanin mutane 20 da ake nema ruwa a jallo dangane da lamarin.