Gwamnan Ogun Abiodun ya baiwa iyalan ƴan wasan Kano da su ka rasu a hatsarin mota Naira Miliyan 31

0
242
Gwamnan Ogun Abiodun ya baiwa iyalan ƴan wasan Kano da su ka rasu a hatsarin mota Naira Miliyan 31

Gwamnan Ogun Abiodun ya baiwa iyalan ƴan wasan Kano da su ka rasu a hatsarin mota Naira Miliyan 31

Daga Jameel Lawan Yakasai

Gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun, a ranar Lahadi ya aike da tawaga zuwa Jihar Kano domin yi wa gwamnatin jihar da al’ummar Kano ta’aziyya bisa rashin wasu ‘yan wasa da jami’ai da suka rasu yayin dawowa daga gasar wasanni ta kasa da aka kammala kwanan nan.

Gwamna Abiodun ya kuma ba da gudummawar Naira miliyan daya (N1m) ga kowanne iyali daga cikin iyalan mamatan a matsayin taimako na farko, wanda jimillar kudin ta kai Naira miliyan 31.

A cewar wata sanarwa da aka fitar a ranar Lahadi, mataimakiyar gwamna, Injiniya Noimot Salako-Oyedele ce ta jagoranci tawagar, da ta haɗa da Sakataren Gwamnatin Jihar Ogun, Mista Tokunbo Talabi; Kwamishinan Ci gaban Wasanni, Hon. Wasiu Isiaka; da Sakataren Gudanarwa na Kwamitin Shirya Gasar wasanni ta kasa Dr. Kweku Tandoh.

KU KUMA KARANTA:An samu mutuwar Yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na Jihar Kano sakamakon hatsarin mota

Tawagar ta iso Kano da misalin ƙarfe 9 na safe, inda mataimakin gwamnan Jihar Kano, Aminu Abdusalam Gwarzo, tare da wasu jami’an gwamnatin Kano suka tarbe su.

Yayin da ta ke bayyana jimamin Gwamna Abiodun kan wannan musiba, Salako-Oyedele ta miƙa sakon ta’aziyya ga gwamnatin Jihar Kano.

Ta ce:”Mun san cewa gwamnan yana wajen aikin Hajji a yanzu, amma mun ga ya dace mu zo da kanmu domin nuna goyon bayanmu ga Gwamna, Gwamnati da al’ummar Jihar Kano a wannan lokaci na jarrabawa.

“Wannan babban rashin da ya shafi Jihar Kano ne, masu ruwa da tsaki a fannin wasanni gaba ɗaya, musamman dangin mamatan da abokan arzikinsu. Muna kuma addu’ar Allah ya ba wa waɗanda ke kwance a asibiti lafiya cikin gaggawa.

Leave a Reply