Yan Daba sun shiga gidansu wani matashi sun kashe shi a Jihar Kano
Daga Jameel Lawan Yakasai
An shiga zaman ɗar-ɗar s Madigawa da kewayenta sakamakon hallaka wani matashi Khalifa Kifaya’u da yan daba suka yi.
KU KUMA KARANTA:An dawo da tsohon jami’in ‘Anti-Daba’ Gwadabe don kakkaɓe ‘yan daba a Kano
Rahotonni sun ce yan dabar sun kutsa kai gidansu matashin da ke Kuka Bulukiya, Madigawa a Ƙaramar Hukumar Dala inda suka hallaka shi.
Yankin dai na cikin yankunan da ake yawan samun fadace-fadacen daba a Kano.