Gwamnatin Tarayya ta sanar da ranakun hutun Babbar Sallah
Daga Jameel Lawan Yakasai
Gwamnatin Tarayya ta ayyana Juma’a, 6 ga Yuni, da Litinin, 9 ga Yuni, 2025, a matsayin ranakun hutu domin bikin Sallah Babba na bana.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da hakan a madadin Gwamnatin Tarayya a cikin wata sanarwa da Babbar sakatariya ta ma’aikatar, Magdalene Ajani, ta fitar a ranar Litinin.
KU KUMA KARANTA:Khuduba: An koma cin mutuncin addini da Malamai da Shugabanni ta hanyar amfani da sabuwar fasahar AI a duniya – Sheikh Sudais
Tunji-Ojo ya taya daukacin al’ummar Musulmi na cikin gida da na kasashen waje murnar wannan lokaci mai albarka.
Ya bukaci al’ummar Musulmi da su ci gaba da ɗaukar darasin sadaukarwa da gaskiya da Annabi Ibrahim (A.S) ya nuna, tare da amfani da wannan lokaci wajen yin addu’a domin zaman lafiya da ci gaban Najeriya.