Tinubu ya ƙaddamar da sabbin jiragen yaƙi masu sauƙar ungulu
Daga Idris Umar, Zariya
A wani ɓangare na kokarin sabunta tsarin tsaron ƙasa. Shugaba Tinubu ya wakilta mataimakinsa Kashim Shettima wajen Ƙaddamar da Sabbin jiragen yaƙin
Shettima ya jaddada kudirin gwamnatin Najeriya na shiga dumu-dumu hannun cikin harkar inganta sabbin fasahohin aiyukan tsaron ƙasa domin wadata sojojin Najeriya da abubuwan da suka dace don tunkarar kalubalen tsaro.
KU KUMA KARANTA: ’Yan Najeriya su ƙara haƙuri kan matakan da muke ɗauka — Tinubu
Gwamnatin ta kuma tabbatar wa da hukumar sojojin saman Najeriya ta NAF da cewa za ta sami ƙarin jiragen yaƙi sama 49 a cikin shekaru biyu masu zuwa.










