NBA ta yi Alla-wadai da dakatar da shirye-shiryen siyasa kai tsaye a Kano

0
61
NBA ta yi Alla-wadai da dakatar da shirye-shiryen siyasa kai tsaye a Kano

NBA ta yi Alla-wadai da dakatar da shirye-shiryen siyasa kai tsaye a Kano

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Ƙungiyar Lauyoyi ta ƙasa (NBA) ta yi watsi da matakin dakatar da shirye-shiryen siyasa kai tsaye a gidajen Rediyo da Talabijin na jihar Kano.

Wannan na cikin wata sanarwa da Shugaban Kungiyar Lauyoyin Mazi Afam Osigwe, SAN ya fitar.

Kungiyar ta bayyana matakin a matsayin take hakkin ‘yancin fadar albarkacin baki da tsarin mulkin kasa ya tanada.

Sanarwar ta ce ba wani gwamna ko gwamnatin jiha da ya ke da ikon tsara ko hana shirye-shiryen yada labarai a kasar nan.

KU KUMA KARANTA: Wata babbar Kotu a Kano ta yi watsi da bukatar Ganduje

Ta ce, wannan hakki ne da ya rataya a kan Hukumar Kula da Kafafen Yada Labarai ta Kasa (NBC), wadda ke da alhakin tabbatar da cewa shirye-shiryen sun dace da dokokin kasa da na kundin tsarin mulki.

NBA ta ce hana shirye-shiryen siyasa ya ci karo da sashi na 39 na kundin tsarin mulkin Najeriya wanda ya tabbatar da ‘yancin fadar albarkacin baki da samun bayanai ba tare da tsangwama ba.

Kungiyar lauyoyin ta ce, wannan mataki zai kawo cikas ga yancin yada labarai a kasar nan.

NBA ta nemi gwamnatin Kano ta janye umarnin hana shirye-shiryen, sannan ta nemi hukumar NBC ta tashi haikan wajen tabbatar da aikinta.

WAIWAYE: A makon da ya gabata ne maʼaikatar yada labaran Kano ta sanar da cewa ta haramta shirye-shiryen siyasa kai tsaye a kafafen yada labaran jihar lamarin da ya janyo kace-nace.

Sai dai gwamnatin ta musanta daga baya, inda shugabannin kafafen yada labaran jihar ta bakin shugaban tashar Freedom Radio Kano Malam Ado Saʼid Warawa suka ce su ne suka yi matsayar ba gwamnatin ba.

Leave a Reply