Gwamnatin Kano ta kama dabbobin da su ke cinye bishiyoyin da aka dasa a sabbin tituna
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi ta Jihar Kano ce ta kama wasu awaki da su ke cinye bishiyoyin da aka dasa don ƙawata sabbin titunan da ake yi a cikin birnin jihar.
Kwamishinan ma’aikatar, Dr. Dahir M. Hashim ne ya baiyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Kano, inda ya ce tuni aka kama wajin aka daure su a ofishin Ƴansanda na Zone 1.
Ya zargi al’umma da sakin wani sakaka, inda ya ce gwamnati ba za ta lamunci hakan ba.
“Mun samu rahotanni cewa wasu suna barin awaki suna yawo suna cin sababbin bishiyoyin da muka dasa.
KU KUMA KARANTA:Kotu a Kano ta tura matasan da suka yi yunƙurin hana zance a Unguwar Ja’en Gidan Yari
“Ina so jama’a su sani cewa wannan abu ne da ba za mu lamunta ba. A halin yanzu, mun kama wasu awaki suna cin bishiyoyin da aka dasa kuma mun ɗauresu a Zone 1,” a certain Kwamishina.
Ya ce a cigaba da aikin da gwamnatin ke yi mai taken UrbanRenewalProject, ma’aikatar ta dasa bishiyoyi a kan titin Lodge Road da Race Course.
Wannan aiki, in ji Kwamishinan, zai ci gaba har sai an dasa bishiyoyi a duk manyan titunan jihar, domin rage zafi da gurbatacciyar iska, tare da ƙawata birnin Kano.
“Muna kira ga jama’a da su bamu haɗin kai don tabbatar da nasarar wannan aiki,”