Ana zargin wani matashi da makantar da saurayin budurwarsa a Kano

0
230
Ana zargin wani matashi da makantar da saurayin budurwarsa a Kano

Ana zargin wani matashi da makantar da saurayin budurwarsa a Kano

Daga Shafaatu Dauda Kano

Kotun shari’ar musulunci mai lamba 1, da ke zamanta a unguwar Fagge ‘yan Alluna ta jihar Kano, ta fara sauraron shari’ar wani matashi da ake zargin ya makantar da saurayin Budurwasa.

Lamarin ya faru ne a ƙaramar hukumar Dawakin Kudu, inda ake zargin Matashin, Abdurrashid Lawan, da makantar da abokin takarar sa, Muhammad Inuwa, saboda wani saɓani da ya shiga tsakanin su akan Budurwarsa.

Kuma dai zargin ya yi ƙarfi akan Abdurrashid ne a sakamakon kalaman da aka ce ya yi, na cewa abokin takarar tasa zai ga abin da zai sameshi, wanda kuma bayan kwana biyu sai ya makance.

To sai dai bayan me gabatar da kara kuma lauyan gwamnati, Barista Zaharaddin Mustafa, ya karanta masa kunshin tuhumar nan take ya musa, mafari kenan da Kotun ta bada umarnin a kai me karar Asibitin kwararru na Murtala dake Kano domin a duba halin da Idon yake ciki.

KU KUMA KARANTA:Neman shahara: Hukumar Hisbah a Kano ta kama matashi da ya shinshini al’aurar akuya

A karshe Alƙalin Kotun, Ustaz Umar lawan Abubakar, ya dage shari’ar zuwa 18 ga watan Mayu me kamawa domin dorawa daga inda aka tsaya.

Bayan fitowa daga kotun, munji ta bakin wanda akai kara Abdurrashid, inda ya ce sharri ake kokarin yi masa domin babu wani asiri da ya yi wa abokin takarar tasa.

Haka kuma Abdurrashid ya ce makantar wanda ya yi karar tasa tana tashi ne a lokacin da za’a je wurin ‘yan sanda ko kuma Kotu, amma da zarar ya koma gida sai ya ci-gaba da harkokinsa ciki har da hawa Keke.

Ko da muka waiwayi me kara Muhammad Inuwa, wato wanda ya ke zargin an makantar da shi ta hanyar asiri, hakar mu ta gaza cimma ruwa domin kuwa ya ki cewa uffan akan shari’ar.

Leave a Reply