Neman shahara: Hukumar Hisbah a Kano ta kama matashi da ya shinshini al’aurar akuya
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Jami’an hukumar Hisbah ta jihar Kano sun kama wani matashi dan shekara 24, wanda ya fito a wani bidiyo ya na ‘lasar’ al’aurar akuya, domin neman shahara a shafukan sada zumunta.
Wakilin Jaridar Neptune Prime a Kano ya ruwaito cewa an kama yaron ne mai suna Shamsu Yakubu, mazaunin karamar hukumar Dawakin Kudu da ke jihar a ranar Talata.
A cikin faifan bidiyon, wanda ya yadu a shafukan sada zumunta, musamman Tiktok, an ga Yakubu yana umurtar wani da ya dauki hotonsa yana a kan lasar al’aurar dabbar .
Ya bayyana cewa ya yi hakan ne saboda yana neman daukaka a shafukan sada zumunta.
Sai dai mazauna yankin da suka fusata da wannan mummunar dabi’ar ta Yakubu, sun yi yunkurin yi masa dukan tsiya, wanda hakan yasa wani mutum a yankin ya mika matashin ga Hukumar Hisbah, inda nan take ta kama shi.
Sai dai a wata tattaunawa da jami’an Hisbah a birnin Kano, Matashin ya musanta cewa ya lashi al’aurar dabbar, inda ya ce ya dora bakinsa ne kawai a al’aurar akuyar.
“Na rantse da Allah ban lashi al’aurar akuya ba, kawai na sanya bakina a wajen,” a cewar sa.
KU KUMA KARANTA:Hukumar Hisbah a Kano ta haramta wasan tashe a faɗin Jihar
“Ban taba yin irin wannan abu a baya ba, ina cikin hayyacina, wannan ne karo na na farko kuma ba zan sake yin hakan ba, a cewar sa,
Sai dai hukumar Hisbah ta ba da umarnin a yi wa matashin gwajin kwakwalwa ko yana da tabin hankali.
Matashin ya kuma ce shi baya shaye-shayen miyagun kwayoyi.
Da yake zantawa da manema labarai kan batun, Mataimakin Babban Kwamandan Hukumar Hisbah, Sheikh Aminuddeen Abubakar, ya ce kafin a hukunta matashin za a yi masa gwaji kwakwalwa don tabbatar da cewa yana cikin hayyacin sa.
“Abin bakin ciki ne mutum musulmi ya yi amfani da bakinsa wajen lasar al’aurar akuya, ba tare da la’akari da koyarwar addini da kyawawan dabi’u ba,” a cewar sa.
A cewar Sheikh Aminuddeen wanda ake zargin bai san komai ba game da addinin musulunci duk da kasancewarsa musulmi.
Ya ce hukumar Hisbah ba za ta saurarawa duk wadanda suke sabawa koyarwar addinin musulunci da sunan neman daukaka ba.