No menu items!

Sample Page Title

Date:

Zargi: ’Yansanda sun musanta sace tsohon kwamishinan El-Rufai

Rundunar ’Yansandan jihar Kaduna, ta ƙaryata zargin da tsohon gwamna Nasir El-Rufai ya yi cewa jami’an tsaro sun sace tsohon Kwamishinansa, Jafaru Sani.

El-Rufai ya yi wannan iƙirari ne a shafinsa na sada zumunta cewa an ɗauke tsohon Kwamishinan kamar fursuna ba tare da bin ƙa’idojin doka ba.

Ya yi zargin cewa wata “ƙungiyar masu garkuwa da mutane” da ke da alaƙa da Gwamna Uba Sani ce ke da alhakin ɗauke tsohon Kwamishinan.

Da yake mayar da martani, kakakin ’yan sandan jihar, DSP Mansir Hassan, ya bayyana zargin a matsayin ƙarya.

KU KUMA KARANTA:An kawo sabon Kwamishinan ‘yansanda a Kano

“Babu wata ƙungiyar masu garkuwa da mutane a cikin Rundunar ’Yan Sandan Najeriya.

“Mu hukuma ce da ke aiki bisa kundin tsarin mulki don tabbatar da doka da oda,” in ji shi.

Ya buƙaci ’yan siyasa su guji yaɗa labaran da ba su da tushe.

“Yi wa jami’an tsaro ƙarya na iya haifar da ruɗani da kuma rage martabarsu. Idan mutum yana da ƙorafi, ya bi hanyar shari’a maimakon yaɗa kalaman da za su tayar da fitina,” a cewarsa.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...