Ambaliyar ruwa ta raba mutane 100,000 da matsugunansu a Burundi

0
170

Gwamnatin Burundi da Majalisar Ɗinkin Duniya sun kaddamar da asusun neman taimakon kudade don magance radadin da mamakon ruwan sama na watanni da ya janyo ambaliya ya haifar ga kusan mutane 100,000.

A ‘yan makonnin nan Gabashin Afirka na fuskantar mamakon ruwan sama da ya janyo asarar rayuka 58 a Tanzania a farkon watan Afrilu, da kuma wasu mutane 13 a Kenya.

Burundi, ƙasar da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce tana ɗaya daga ƙasashen 20 da sauyin yanayi ya fi illatawa, na fuskantar ruwan sama tun watan Satumban bara inda babban birninta Bujumbura ya fuskanci ambaliya sosai.

Mamakon ruwan saman da ake samu saboda tasirin El Nino na janyo mummunar ambaliyar ruwa sakamakon cika da koguna ke yi da kuma karyewar Tafkin Tanganyika.

Zaftarewar ƙasa, iska mai karfi tare da ruwan kankara na ci gaba da yin barazana ga al’ummu, in ji wata sanarwar haɗin gwiwa da Ministan Harkokin Cikin Gida Martin Niteretse da babban jami’in MƊD Violet Kenyna Kakyomya suka fitar.

A tsakanin Satumba da 7 ga Afrilu, jimillar mutane 203,944 ne lamarin ya rutsa da su, inda waɗanda aka tsugunar suka ƙara yawa da kaso 25 inda suka kama dubu 96,000.

A sanarwar da aka bayar game da asarar rayuka ba a yi cikakken bayani ba, an bayyana rasa rayuka da dama, lalacewar gonaki da amfanin gona da rushewar guidaje.

Gwamnatin Shugaba Evariste Ndayishimiye na ta fuskantar matsin lamba daga ƙungiyoyin sa-kai da ‘yan adawa, inda suka buƙaci ta ayyana doka ta-ɓaci.

KU KUMA KARANTA: Ambaliyar ruwa ta kawo gagarumin tsaiko a sufurin jiragen sama a Dubai

Akasari akwai lokutan damuna guda biyu a Burundi tsakanin Satumba da Janairu da kuma Maris zuwa Mayu, amma tasirin yanayi na El Nino ya sake munana lamarin.

Hasashen yanayi ya bayyana cewa za a ci gaba da samun ruwan sama kamar da bakin kwarya har nan da watan Mayu “gwamnati da masu bayar da agajin gaggawa na bukatar kuɗaɗe da kayan aiki don fuskantar ƙalubalen da ke daɗuwa da kuma magance taɓarɓarewar lamarin,” in ji sanarwar ta hadin gwiwa.

Sanarwar ta kuma ce mutane 306,000 na cikin halin buƙatar jinkai da gaggawa a Burundi, ƙasar da Bankin Duniya ya bayyana a matsayin mafi talauci duba da kuɗaɗen da take samu a cikin gida.

A babban birnin kasuwanci na Bujumbura, wanda ke kwance a gabar arewa maso-gabashin Tafkin Tanganyika, unguwanni da dama sun malale da ruwa, hanyoyi da gadoji sun karye, an bar gidajen otel da asibitoci saboda cikar ruwa a cikin su.

Matakin ruwan a ƙasa ta biyu da ta fi kowacce tafki mai girma a Afirka, ruwan ya kai tudun mita 77.04 a ranar 12 ga Afrilu, sentimita ƙasa da girmamar da ya yi a 1964, in ji shugabar hukumar agajin gaggawa Anicet Nibaruta a ranar Juma’a, kamar yadda kafafan yada labarai na Burundi suka rawaito.

El Nino na da mummunan sakamako a Gabashin Afirka, inda a Disamba kawai sama da mutane 300 suka mutu bayan mamakon ruwan sama a Kenya, Somalia da Ethiopia.

Daga Oktoban 1997 zuwa Janairun 1998, mamakon ruwan sama ya janyo mutuwar sama da mutane 6,000 a ƙasashe biyar na yankin.

Leave a Reply