Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya karrama sojojin Najeriya da aka kashe a Jihar Delta lambar yabo da girmamawa ta kasa na MON da OFR.
Tinubu ya ayyana bai wa dakarun sojin da suka riga mu gidan gaskiya lambobin yabon ne yayin jana’izarsu a maƙabartar sojojin da ke Abuja a ranar Laraba.
Ya ce, manyan sojojin huɗu daga cikin wadanda aka kashe ya ba su lambar yabo ta MON, yayin da su kuma kananan sojojin goma sha uku an ba su lambar yabo ta OFR.
Tinubu ya kuma bai wa shugabannin kabilar Okuama umurnin bayyana waɗanda suka aikata wannan mummunan aiki ga dakarun sojin a Jihar Delta
Ya ce, “Ina so in ƙara jaddada cewa waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki dole za su fuskanci hukunci . Za mu kamo su kuma za a yi wa dakarunmu da suka rasu adalci.
KU KUMA KARANTA: Rundunar sojin Najeriya na neman mutum takwas ruwa-a-jallo kan kisan dakarunta a Delta
“Ya zama wajibi manyan kasa da sarakunan Okuama su taimaka wa sojoji wurin kamo ɓata-garin da suka aikata wannan aika-aika ga dakarun mu.
“Ina so in yaba wa sojojinmu kan yadda suka kau da kai, suka danne zuciyarsu, ba su kai wani hari na ramuwar gayya a kan jama’ar Okuama ko kuma makwabtansu ba
“Dole ne mu tabbatar da cewa ba a sanya mutanen Okuama da ba su ji ba su gani ba ɗaukar hukuncin masu laifi da miyagu daga cikinsu.
“Gwamnatin Tarayya za ta samar da gida ga iyalan manyan sojojin huɗu da da kuma kananan sojojin 13 da aka kashe.
“Gwamnatin Tarayya ta kuma amince da bayar da ɗauka nauyin karatu ga duk ’ya’yan waɗanda suka rasu har zuwa jami’a.”
A karshe ya ce, “dole ne sojoji su tabbatar da cewa an biya duk wani haƙƙi na magada nan da kwanaki casa’in masu zuwa.”
An kashe sojojin ne dai a yankin Okuama da ke Ƙaramar Hukumar Ughelli ta Kudu a Jihar Delta, yayin da suka amsa kiran gaggawa domin kawo kwantar da wata tarzomar sakamakon rikicin da ya ɓarke kan fili a tsakanin al’ummar yankin.