Sama da mutane shida ne suka samu munanan raunuka a harbin jirgin ƙasa a New York

Ma’aikatan kashe gobara sun ce mutane shida sun jikkata, kuma mutum ɗaya daga cikinsu na cikin mawuyacin hali sakamakon harbin da aka yi a tashar jirgin karkashin ƙasa a birnin New York da yammacin jiya Litinin.

KU KUMA KARANTA:Sarkin Kano ya aika wa Tinubu saƙo kan wahalar da jama’a ke ciki

Hukumar kashe gobara ta ce an sanar da hukumomi da misalin ƙarfe 4:30 na yamma (agogon GMT 2130) game da harin, kuma tuni aka kai marar lafiya ɗaya da ke cikin mawuyacin hali zuwa asibiti, kamar yadda ma’aikatar kashe gobara ta bayyana. Ba a bayar da dalilin yin harbin ba.

Hare-hare kan jama’a sun zama ruwan dare a Amurka, inda ake da bindigogin da suka fi jama’a yawa kuma kusan kashi uku na Amurkawa manya sun mallaki bindiga.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *