Abubuwan fashewa sun kashe mutane 26 a kusa da ofisoshin ‘yan takara a Pakista

Wasu fashe-fashe guda biyu a kusa da ofisoshin ‘yan takara a lardin Balochistan na kudu maso yammacin Pakistan sun kashe mutane 26 tare da jikkata wasu da dama, a cewar jami’an yankin a ranar Laraba 7 ga watan Fabrairu, lamarin da ya ƙara nuna damuwa kan tsaro a jajibirin babban zaɓe. Pakistan za ta kaɗa ƙuri’a a ranar Alhamis 8 ga watan Fabrairu; a daidai lokacin da ake samun ƙaruwar hare-haren ‘yan bindiga a cikin ‘yan watannin nan da kuma tsare Imran Khan, wanda ya lashe zaɓen ƙasar da ya gabata, wanda ya mamaye kanun labarai duk da rikicin tattalin arziƙi da wasu matsaloli da ke barazana ga ƙasar mai makaman nukiliya.

Hukumomin ƙasar dai sun ce suna ƙarfafa matakan tsaro a rumfunan zaɓe. Harin farko wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 14, an kai shi ne a ofishin ɗan takarar zaɓe mai zaman kansa a gundumar Pishin.

KU KUMA KARANTA:‘Yansandan a jihar Neja sun kama matan da ake zargin sun shirya zanga-zangar tsadar rayuwa

Fashewar na biyu a garin Qila Saifullah da ke kusa da kan iyaka da Afganistan ya tarwatse ne a kusa da ofishin Jamiat Ulema Islam (JUI), jam’iyyar addini da a baya ta sha kai hare-hare kamar yadda ministan yaɗa labaran lardin ya bayyana.

Mataimakin kwamishinan Qila Saifullah, Yasir Bazai ya ce mutane 12 ne suka mutu sakamakon fashewar bam ɗin da ta samo asali daga wani babur da aka ajiye a kusa da ofishin, sannan 25 suka jikkata.

Kawo yanzu dai ba a bayyana ko su waye suka kai hare-haren ba.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *