Daga Ibraheem El-Tafseer
Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta shiga zawarcin ƙananan jam’iyyun adawa ciki harda jam’iyar NNPP ta Rabi’u Musa Kwanwkaso da mabiyansa.
Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ne ya shaida wa BBC cewa tuni suka aike da goron gayyata ga gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa Rabiu Musa Kwankwaso.
Ganduje ya yi waɗannan kalamai ne a wani taro da ya jagoranta da shugabannin jam’iyyarsa ta APC a jihar Kano, inda ya ce dama can uwa ɗaya uba ɗaya suke da su Kwankwason.
A cewa Ganduje, “Wannan ya zama dole saboda a matsayina na shugaban jam’iyyar APC na ƙasa ina zagayawa jihohi, sanatoci sun shigo cikin wannan jam’iyya tamu ‘yan majalisar tarayya sun shigo wannan jam’iyya tamu, haka nan kuma gwamnoni.
Shugaban APC ya ce nan gaba ma akwai waɗanda za su shigo cikin jam’iyyar, kuma wannan dalili ne ya sa ya fito yana neman haɗin kai daga jiharsa ta Kano.
KU KUMA KARANTA: Tinubu ya gana da Ganduje, shugabannin APC na Jihar Kano
“Na ma ƙira wasu na waje ballantana namu na gida” in ji shi.
Sai dai shugaban jam’iyyar APC ya ce kawo yanzu ba su rubutawa jagoran jam’’iyyar NNPP da gwamnan jihar Kano wasiƙa a hukumance ba game da wannan ƙiran da suka yi mu su.
A cewarsa suna son ɓangaren Kwankwaso ya nuna sha’awar shiga jam’iyyarsu ta APC kafin a je matakin aike wasiƙa.
Wannan buƙata ta APC na zuwa ne adaidai lokacin da jama’a da dama ke nuna shakku kan ba lallai tafiyar tayi kyau ba tsakanin Kwankwaso da Ganduje a inuwa guda.
Amma Ganduje ya nuna ƙwarin gwiwa tare da tunasar da cewa, “ai dama can gidanmu ɗaya, dama can Ubanmu ɗaya, an samu rarrabuwar kai, yanzu kuma idan Allah ya sake haɗawa, to me ya fi wannan daɗi”.