Hukumar EFCC ta titsiye Akanta-Janar ta Tarayya, AGF, Oluwatoyin Madein tare da kuma gayyatar ƙarin ma’aikatan ma’aikatar jin-ƙai kan zargin badaƙalar N585.2m.
Wata majiya a EFCC ta bayyana cewa an gayyaci Misis Madein da wasu ma’aikatan ne bisa alaƙa da zargin da ake yi na N585.2m da ta shafi ministar jin-ƙai da aka dakatar, Dr Betta Edu.
Majiyar ta ce jami’an EFCC sun yi wa AGF ɗin tambayoyi na tsawon sa’o’i da dama a hedikwatar hukumar da ke Jabi, Abuja amma daga baya aka sake ta.
Majiyar ta ce an tambayi Misis Madein ne kan biyan naira miliyan 585.2 na kuɗaɗen gwamnati daga ma’aikatar zuwa asusun ajiyar banki na wani jami’in gwamnati.
Madein, a cewar majiyar, ta shaida wa masu tambayoyin cewa ba ta sa hannu a kan takardar da ministar, Misis Edu ta aike mata na biyan kuɗin a wani asusu na ƙashin-kai ba.
KU KUMA KARANTA: EFCC ta kama tsohon minista bisa laifin zamba
“An yi mata tambayoyi ne na tsawon sa’o’i da dama a ranar Litinin kan biyan N585.2m daga asusun ajiyar kuɗi na National Social Investment Office (NSIO) zuwa asusun UBA na UBA na Bridget Oniyelu, Akanta na Tallafawa ga kungiyoyi masu rauni a ƙarƙashin ma’aikatar.
“Ta gaya wa masu binciken cewa ba ta saka hannu a takardar da Edu ta tura mata ba don biyan kuɗi a asusu na ƙashin-kai.