Bamu da wani Farfesan bogi a Jami’ar Bayero – Shugaban Jami’ar

0
128

Jami’ar Bayero da ke kano,ta musanta rahoton da ake yaɗawa na cewar an gano farfesoshin bogi har guda 20 a jami’ar.

Jami’ar ta musanta labari ne ta cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, me ɗauke da sa hannun Shugaban Jami’ar Farfesa Sagir Adamu Abbas.

Sanarwar tace ta kula da yadda ake yaɗa wata sanarwar bogi a kafafan sada zumunta, wadda ke cewa an gano farfesa guda 100 na bogi dake aiki a Jami’oin Najeriya.

A saboda haka ba tare da wata shakka ba, muke sanar daku cewa waccan sanarwa da ake yaɗawa, ba komai bace illa mara tushe, wadda wasu suka ƙirƙira domin taɓa martabar jami’ar.

KU KUMA KARANTA: An kama likitan bogi da ke ziyartar asibiti a Zamfara yana duba matsalar al’aurar mata

Haka kuma shugaban jami’ar yayi bitar yadda hukumar dake kula da jami’oin ƙasar, ta tabbatar da cewa waccan sanarwa ta bogi ce.

Sanarwar ta ƙara da cewa ”babu yadda za’ai a sami irin wannan lamari a jami’ar Bayero, duba da yadda muke cikin manyan jami’oin da suke bada ingantaccen ilimi, kamar yadda masu kididdiga akan jami’oin duniya suka tabbatar”.

A ƙoƙarin kauda shakku daga zukatan Al’umma, Jami’ar tace ko a baya-bayan nan ta zama ta biyar a sahun jami’oi masu inganci a Najeriya, a fannin bincike,bada horo dama ingantaccen tsarin koyo da koyarwa.

Haka kuma Jami’ar ta zama ta biyu a Najeriya a ɓangaren waɗanda tsarukan su yayi dai-dai da na ƙasashen duniya, wanda kuma hakan ya faru ne a sakamakon ingantaccen ilimin dama samar da ɗaliban da sukayi zarra a tsakanin sa’oinsu.

A karshe Jami’ar tayi fatan Al’umma zasu yi watsi da waccan sanarwa da ake yaɗawa.

Leave a Reply