No menu items!

Sample Page Title

Date:

Wasu mata sun samu kansu a cikin damuwa bayan da sababbin ’yan hayar gidansu suka tsere da ’ya’yansu huɗu, kwana uku da kama haya a gidan da suke a Umahiya fadar Jihar Abiya.

’Yan hayar da aka sace wa ’ya’yan, Ngozi Kingsley da Madam Ifeyanyi Uduma ’yar uwar Ngozi Kingsley da Blessing Peter Obasi daga gidan Nwoke da ke Enugwu, Nguzu Edda a Jihar Ebonyi dukkansu suna kasuwanci ne a Umahiya.

Su bayyana cewa sababbin ’yan hayar mata su biyu waɗanda ba su rike cikakken sunayensu ba, sun tare a gidan da suke haya ne a ranar Alhamis 15 ga Disamban nan a ɗakin da suka karɓa haya da ’yar katifarsu da ƙaramin abin girki na gas da kuma babbar jakar Ghana must-go guda ɗaya.

Sun ce cikin sakin fuska farin ciki da walwala suka ja kowa a jika musamman yaran gidan inda suke ba su abubuwan kwalam da makulashe har da abinci wanda hakan ya sa kowa ya saki jiki da su har yaran suke shiga ɗakin matan suna wasa a cikin kwana biyu da tarewarsu.

KU KUMA KARANTA: Hisbah a jihar Kebbi ta sami ƙananan yara ‘yan mata su biyu suna gararamba a gari

A rana ta uku sai bakin matan suka shammaci iyayen yaran inda ɗaya daga cikin bakin matan ɗauke da babbar jaka cike da kaya ta ce za je unguwa wuri ’yar uwarta ta kai kayan, ta kuma fita a idon ɗaya daga cikin iyayen yaran mai suna Uduma, yayin da ɗaya abokiyar hayarta ke zaune da sauran gidan suna ta wasansu.

Bayan ta tafi sai ɗaya bakuwar ’yar hayar ta ce bari ta je da sauran yaran su sayo biskit a shago sai suka fita, fitar da ba su dawo ba har dare, hakan ya sa aka shiga nemansu da lamarin ya ci tura aka je babban ofishin ’yan sanda aka sanar da su da kuma neman dauki.

Kakakin ’Yan sandan Jihar, Maureen Chinaka wadda ta tabbatar da labarin ta ce, “Yanzu haka sun kama wasu da suke da alaƙa da sababbin ’yan hayar, kuma an fara bincike don gano inda yaran suke.”

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...