No menu items!

Sample Page Title

Date:

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya daidaita rikicin siyasar jihar Ondo da aka kwashe watanni ana fama da ita ɓangaren gwamnan jihar Rotimi Akeredolu da mataimakin gwamnan Lucky Aiyedatiwa.

Cikin wata sanarwar da mai magana da yawun shugaba Tinubun, Ajuri Ngelale, ya fitar ranar Asabar, ya ce an cimma hakan ne bayan kwashe lokaci mai tsawo ana tattaunawa tsakanin ɓangarorin biyu da ‘yan majalisar jihar da ɓangaren jam’iyyar APC na jihar, da kuma shugaban ƙasar ranar Juma’a a fadarsa da ke Abuja.

Sanarwar ta ce shugaba Tinubu ya shawarci duka ɓangarorin da su manta da duka abubuwan da suka faru, domin zaman lafiyar jihar da gudanar da ayyukan ci gaba.

KU KUMA KARANTA: Babu ɗalibin da zai bar makaranta saboda rashin kuɗi a mulkina – Tinubu

Sasancin ya tabbatar da cewa Akeredolu zai ci gaba da zama a matsayin gwamna, yayin Aiyedatiwa zai ci gaba da kasancewa a matsayin mataimaki.

A baya-bayan nan dai an samu rashin jituwa tsakanin majalisar dokokin jihar da mataimakin gwamnan bayan da majalisar ta zarge shi aikata wasu laifuka ciki har da rashin biyayya ga gwamnan jihar.

Lamarin da ya kai har da barazanar tsigewa, inda ya garzaya wata babbar kotu a Abuja wadda ta dakatar da ‘yan majalisar daga yunkurin.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...